Ƴan Sanda A Kano Sun Fara Bincike Kan Zargin Lakaɗawa Wani Likita Duka A Asibitin Murtala

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta soma gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa wasu mutane na dukan wani likita a Asibitin Kwararru na Murtala da ke cikin Birni.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Litinin da tsakar dare.

‘Yan sandan sun ce bayanan da suka samu sun nuna cewa dangin wata mata mai juna biyu ne suka lakada wa likitan mai suna Shehu Usman Abdulwahab duka bayan ta mutu a yayin da yake karbar haihuwa.

Wannan lamari ya tayar da yamutsi a Asibitin kuma “bayan samun wannan rahoto ne aka tura tawagar ‘yan sanda wurin da lamarin ya faru nan-take,” a cewar Kiyawa.

Ya kara da cewa daga bisani Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Mohammed Usaini Gumel ya ziyarci asibitin inda ya gana da jami’ai da masu ruwa da tsaki domin ganin halin da ake ciki.

“Ya tabbatar musu cewa rundunar ‘yan sandan Kano tana daukar lamarin da matukar muhimmanci kuma tuni ta soma bincike a kansa. Kwamishinan ya umarci a kai karin jami’ai domin tabbatar da tsaro a Asibitin,” in ji kakakin rundunar ‘yan sandan.

Kiyawa ya ce “rundunar ‘yan sandan Kano ba za ta lamunci duk wani cin zarafi da barazana ga ma’aikatan kiwon lafiya ba wadanda suke yin aiki babu dare babu rana domin ceto rayukan jama’a da kula da marasa lafiya”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories