spot_imgspot_img

Nan Da Kwanaki Biyar A Tsammaci Wutan Lantarki – Minista Ya Magantu

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, a yau Litinin, ya ce nan ba da jimawa ba za a dawo da wutar lantarki a jihohin Arewa 17 da suke fama da matsalar Lalacewar wuta.

KU KARANTA : Ya Kamata A Yiwa Lalacewar Wuta Tufkar Hanci A Najeriya – Kwankwaso

 Mista Adelabu ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa biyo bayan wata ganawa da yayi da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar sa da ke Abuja.

 Ministan Ya ce matsalar wutar lantarki da aka fuskanta a yankin Arewacin kasar nan ya samo asali ne biyo bayan Lalacewar  layin wuta daga Shiroro zuwa Kaduna, wanda shi ne babban layin da ke samar da wutar lantarki ga Arewacin Najeriya.

 Sai dai Ministan ya bada tabbacin cewa nan da kwanaki uku zuwa biyar wuta zai samu.

 “A yanzu haka Shugaban kasa ya umurci mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), shugaban hafsan tsaro, hafsoshin soji, shugaban hafsan sojin sama, da su samar da cikakken tsaron da ake bukata ga mutanen da zasu yi aikin gyaran Lalacewar Wutar.

Ministan ya ce indai Za a samar da cikakken tsaro, ma’aikatan TCN tare da ‘yan kwangila, tabbas za su sami kwarin gwiwar tsayawa yin gyara yadda ya kamata.

 Ministan ya kara da cewa“ Ƴan’uwanmu maza da mata,da iyayen mu na Arewacin kasar nan ina kira da, da su yi hakuri da mu, nan ba da jimawa ba za a dawo da wuta, kuma yana da kyau mu hada kai mu kare tattalin arzikin kasa domin kauce wa barna,”  .

 A yanzu haka ministan ya ce majalisar zartaswa ta tarayya ta amince wa ma’aikatar wutar lantarki da ta inganta layin wuta daga Shiroro zuwa Kaduna, kasancewar yana daya daga cikin tsofaffin layukan wuta a Najeriya.

 Daga zarar an gyara wannan matsalar, yankin arewa za ta samu isasshen wuta fiye da yadda ake samu a da.

 Ya kuma yi alkawarin kiran taron ganawa da shugaban hukumar kula da samar da wutar lantarki ta Najeriya NERC, da kuma dukkan kamfanonin rarraba wutar lantarki (DISCO) domin tabbatar da cewa al’ummar yankin Arewa basu biya kudin wutan kwanakin da ba su sha wuta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories