spot_imgspot_img

‘Yan Bindiga Sun Kwace Iko Da Babban Sansanin Horar Da Sojojin Nigeria

Manoma daga garuruwa 23 sun gudu sun bar muhallansu bayan ‘yan bindiga sun karbe iko da sansanin horon soji mafi girma na Nigeria da ke jihar Niger.

Rahotanni sun bayyana cewa sansanin horon sojojin, wanda ya mamaye wani yanki na karamar hukumar Kontagora da karamar hukumar Mairiga, ya koma karkashin ikon ‘yan ta’adda dauke da manyan bindigu.

Akwai fargabar cewa barin garuruwansu da manoman su ka yi zai iya haifar da karancin abinci a Nigeria.

Labarin wannan abin takaici ya fito ne daga bakin mamba a majalisar dokoki ta jihar Niger yayin da ya gabatar da batun a zauren majalisar domin su tattauna halin da sansanin horon sojoji na Nagwamase a karamar hukumar Kontagora ya ke ciki.

A cewar mambobin majalisar, kwace iko da sansanin sojin ya sake haifar da sabuwar barazanar tsaro ga jami’an rundunar soji da sauran jama’a da ke zaune yankin.

KARANTA: Zamfara: Sojoji sun kashe Jagororin ‘Yan Bindiga Biyu; ‘Black’ Da Kachalla

KADUNA: Jama’a Sun Kone Gawarwakin ‘Yan Bindiga a Kachia

Nigeria Za Ta Ci Bashin $16m Domin Siyo Jiragen Yaki 6 Daga Kasar Italy

Abdullahi Isah, mamba mai wakiltar mazabar Kontagora II, shine wanda ya gabatar da kudirin neman majalisar ta gaggauta daukan mataki a kan lamarin.

Ya kara da cewa zaman ‘yan bindiga a sansanin sojojin ya kara yawan adadin hare-haren da ake kai wa garuruwan da su ke makwabta da sansanin, lamarin da ya tilasta jama’a guduwa daga gidajen su domin neman mafaka.

Majalisar ta nuna damuwa a kan yadda ‘yan bindigar su ka mayar da muhimmin wurin bawa sojoji horo na Nagwamase sansanin su. Sansanin ya kasance wuri na musamman domin bawa sojoji horo kafin tura su wuraren da za su yi aiki a fadin Nigeria.

‘Yan majalisar sun yi kira ga gwamnatin jihar Niger a kan ta gaggauta daukan mataki domin ganin an fatattaki ‘yan bindigar domin zaman lafiyar mazauna yankin har ma da jami’an tsaro.

Naziru Taura
Naziru Taurahttp://wikkitimes.com/hausa
Naziru Taura is a dedicated teacher, Hausa blogger, freelancer, and translator with a passion for education, information dissemination, and purposeful leadership. He specializes in crafting compelling stories in both English and Hausa, focusing on the Sustainable Development Goals (SDGs) and amplifying the voices of marginalized and underreported communities. Through his work, Naziru offers hope, advocates for justice, and drives meaningful conversations on societal progress. With over a decade of experience, Naziru has produced numerous impactful stories, shedding light on business and economic empowerment opportunities. His investigative work has also uncovered cases of corruption, abuse of power, and the mismanagement of public funds, showcasing his commitment to accountability and transparency.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories