spot_imgspot_img

Wata Kotu A Jos Ta Yankewa Makiyayi Hukuncin Daurin Wata 9 A Gidan Yari

Kotun Majistare a Jos ta Yanke wa Makiyayi Hukuncin Wata Tara a Kurkuku Saboda Dukan Wata Mace

A ranar Alhamis, wata kotun Majistare a Jos ta yanke wa wani makiyayi mai shekaru 41 mai suna Isa Mohammed hukuncin wata tara a gidan yari saboda dukan wata mace.

Alkalin Kotun Majistare Shawomi Bokkos ne ya yi shari’ar ta gaggawa kuma ya yanke masa hukunci bayan ya amsa laifin da aka tuhume shi da shi.

KARANTA WANNAN: Bauchi: Kotu Ta Yankewa Mutumin Da Ya Yiwa Yarinya Fyaɗe A Masallaci Ɗaurin Rai Da Rai

Kotu Ta Kori Kakakin Majalisar Dokokin Filato

Kotu Ta Ba Da Belin Likitan Da Ke Saida Sassan Jiki A Jos

Bokkos, wanda ya yanke masa hukuncin wata tara a gidan yari, ya ba shi zabin biyan tarar N50,000 tare da biyan diyyar N30,000 ga mai shigar da kara.

Tun da farko, mai gabatar da kara, Insifeta Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotu cewa an kai karar ne a ranar 27 ga watan Agusta, a ofishin ‘yan sanda na “C” Division da ke Jos, daga Hassana Sambo, wacce ita ce mai shigar da kara.

Gokwat ya ce wanda ake tuhuma ya doki matar sannan ya lalata wayarta wadda kudin ta ya kai N45,000.

Ya ce laifin ya saba wa kudin laifuka da hukunce hukuncen su  na jihar Filato. (NAN)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories