Gwamnatin Tarayya ta nemi yafiyar daukewa wuta lantarki na kimanin makonni biyu da aka yi a Arewacin Najeriya, tare da tabbatar wa al’umma cewa faruwar hakan ba da gangan ba ne.
KU KARANTA : Yanzu Yanzu : Wutan Lantarki Ya Dawo A Jihohin Arewa Huɗu
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, shi ne ya bayyana haka a wata ziyara da ya kai hedkwatar kamfanin rarraba wutar lantarki da ke Kano (KEDCO) a jiya Alhamis.
Ministan ya bayyana cewa dauke wutar lantarki da ya faru ba da gangan ba ne, lamarin ya faru ne ba zato ba tsammani.
Haka kuma Ministan Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnati ta dukufa wajen ganin ta magance wannan matsalar tare da maido da cikakken wutar lantarki nan ba da jimawa ba.
“Abin da ya faru a cikin ‘yan kwanakin nan be yi dadi ba, a yi hakuri Muna fatan hakan ba zai sake faruwa ba. “
“Idan an gyara,za mu yi tunanin hanyar samar da wutar lantarki don tabbatar da cewa gidaje da kasuwanci sun daina fuskantar daukewar wuta.A karshe ku sani cewa abinda ya faru ba da gangan ba ne.”
“Ba da gangan ba ne. Bamu da wani Ƙudurin maida wani yanki na kasar nan saniyar ware. Shugaba Bola Ahmad Tinubu na kowa ne.”
“Dukkanmu mun fito mun zabe shi. Kuma bai ji dadin faruwar wannan lamari na dauke wuta ba shiyasa nan take ya bada umurnin a fara gyara a dawo da wuta.



