Jihohi goma sha bakwai ne a fadin Nigeria da har yanzu babu wani labari dangane da shirin da suke yi na fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 da aka amince da shi, lamarin da ya jefa ma’aika a wadannan jihohi cikin fargabar rashin sanin lokacin da zasu fara cin moriyar karin.
Daga cikin wadannan jihohi guda goma sha bakwai, akwai takwas daga cikinsu da suka fito daga yankin arewa wadanda har yanzu babu wata niyya da suka nuna domin karawa ma’aikatan su albashi.
WikkiTimes ta yi tankade tare da rairaya wajen zakulo wadannan jihohi na arewa da suka hada da Bauchi, Kwara, Nasarawa, Plateau, Sokoto, Taraba, Yobe, da Zamfara. Hakazalika, gwamnatin babban birnin tarayya (FCT), Abuja, ba ta bayyana matsayar ta ba.
KARANTA: Yadda Wani Kauye Ya Noma Shinkafa Don Gina Sabon Ajin Makaranta A Bauchi
Bauchi :Â SUBEBÂ Ta Gayyaci Malamai 57Â AKan Fashin Zuwa Aiki
Bayan Barazana Ga Mawallafin WikkiTimes, Dan Gwamnan Bauchi Ya Yi Barazanar Maka Dan Bello A Kotu
Gwamnan Bauchi Ya Yiwa Sarakuna Kyautar Nunawa Sa’a
Har yanzu jihohi kalilan ne suka yi wani hobbasa wajen ganin sun kaddamar da sabon karin albashi daga N30,000 zuwa N70,000 da shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi bayan an kai ruwa rana tsakanin gwamnatinsa da kungiyar kwadago (NLC).
Rahoton WikkiTimes ya bayyana cewa ya zuwa yanzu jihohi 18 ne a cikin 36 suka fara biya ko kuma suka yi alkawarin fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikatansu.
Sauran jihohin Nigeria da har yanzu ba a ji duriyar su dangane da shirin da suke na fara biyan sabon albashin ba sun hada da Ekiti, Edo, Delta, Bayelsa, Akwa Ibom, Imo, Cross River, da Enugu.



