spot_imgspot_img

‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 10, Sun Sace Indiyawa A Jihar Niger

A kalla manoma goma, ciki har da mata, wasu ‘yan bindga suka kashe a kauyukan Wayam da Belu-Belu da ke karkashin karamar hukumar Rafi ta jihar Niger, kamar yadda Daily Trust ta rawaito a ranar Laraba.

Mazauna kauyukan sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun cire kayuwan manoma shida daga cikin wadan da su ka kashe tare da tafiya da su.

Sun kara da cewa mutane da yawa sun samu raunuka daga harbin bindiga kuma a halin yanzu suna samun kulawa a asibitin garin Kagara, hedikwatar mulki ta karamar hukumar Rafi.

Bala Tukur, mazaunin yankin, ya shaidawa wakilin jaridar Daily Trust cewa mazuna kauyukan Wayam, Belu-Belu, da Madaka sun gudu zuwa garin Kagara domin neman mafaka tun da safiyar ranar Talata.

“A kauyen Wayam da ke kusa da Madaka, sun kashe mutane 10 tare da raunata wasu da dama. Su na kashe mutane ba tare da tausayi ba, yanzu duk a firgice mu ke, na rantse. Kowa yanzu ya gudu.

“Har yanzu mutane da yawa ba su girbe kaso 50 na amfanin gonar su ba duk da sun kai matakin girbi amma zuwa wurin yanzu ya gagara.

DUBA WANNAN: ‘Yan Bindiga Sun Kwace Iko Da Babban Sansanin Horar Da Sojojin Nigeria

“A kwanan nan mazauna Kukoki su ka biya tarar N1.5m ga ‘yan bindiga kafin su girbe amfanin gonar da su ka shuka. Amma a hakan ‘yan bindiga su ka sake kai musu hari kwanaki hudu da suka wuce,” a cewar sa.

Hare-haren ‘yan bindiga ya kara zafafa a cikin makon da ya gabata a daidai lokacin da manoma a Wushishi, Rafi, Shiroro, Mariga, da Kontagora su ka fara girbe amfanin gonakin su.

A ranar Juma’a ne Daily Trust ta rawaito cewa ‘yan bindiga sun kai hari garin Zungeru da Wushishi inda su ke bi gida-gida da Otal tare da yin awon gaba da mutane.

Kazalika, Daily Trust ta rawaito cewa an sace wasu Indiyawa biyu a wata gonar shinkafa a yankin Swashi da ke karamar hukumar Borgu a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2024.

Wani mazunin yankin da ya nemi a boye sunansa ya sanar da Daily Trust cewa ‘yan bindga sun kashe daya daga cikin ma su gadin gonar yayin da su ka kai harin.

Kwamishinan tsaron cikin gida a Neja, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed, ya ce gwamnatin jiha ta na da masaniyar kai hare-haren.

“Gwamnatin Jihar Niger ta na sane sarai da abubuwan da ke faruwa. Gwamnati ta sanar da dukkanin jami’an tsaro wadanda yanzu haka sun bazama cikin aiki domin kiyaye afkuwar lamarin a nan gaba”, a cewar sa.

Naziru Taura
Naziru Taurahttp://wikkitimes.com/hausa
Naziru Taura is a dedicated teacher, Hausa blogger, freelancer, and translator with a passion for education, information dissemination, and purposeful leadership. He specializes in crafting compelling stories in both English and Hausa, focusing on the Sustainable Development Goals (SDGs) and amplifying the voices of marginalized and underreported communities. Through his work, Naziru offers hope, advocates for justice, and drives meaningful conversations on societal progress. With over a decade of experience, Naziru has produced numerous impactful stories, shedding light on business and economic empowerment opportunities. His investigative work has also uncovered cases of corruption, abuse of power, and the mismanagement of public funds, showcasing his commitment to accountability and transparency.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories