spot_imgspot_img

Nasarawa: Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Uku

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakon wani rikicin manoma da makiyaya da ya balle a jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar, Umar Nadada, shi ne ya bayyana faruwar lamarin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yau Alhamis a garin Lafiya.

Kwamishinan ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a unguwar Dogon Dutse, da ke tsakanin karamar hukumar Nasarawa da Toto .

A nashi bangaren, Jami’in ‘yan sanda yankin (DPO) ya bayyana cewa ya samu rahoton faruwar rikici tsakanin manoma da makiyaya tun a ranar Litinin da misalin karfe 4:30 na yamma.

 “Ko da muka isa wurin, mun tarar da gawar mutane biyu a gona yayin da wasu hudu suka samu raunuka inda a nan take aka garzaya da su zuwa asibiti.” in ji shi.

KARANTA: Kano: Mutane uku sun rasa ransu sakamakon rikicin kauraye a wurin gangi

Kano: Rikakken Dan Daba, Abba Burakita, Ya Mutu Bayan Artabu Da Yaran Goje A Dorayi

Kano: Ambaliyar Ta Kashe Mutane 49, Ta Shafi Garuruwa 226

Sai dai, Ya ce daga baya ‘yan sandan sun sake samu karin wata gawa a cikin daji a yayin da suke gudanar da bincike.

Kwamishinan ya ce a yanzu haka zirga zirga ya dawo a yankin, inda yace yan sanda na nan su na bincike don gano musabbabin faruwar lamarin.

”A yanzu haka yan sanda sun nemi hadin kan al’umma domin ganin an kamo wadanda ke da hannu wajen aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da sun fuskanci doka.

Haka kuma kwamishinan ya bukaci mutanen yankin da su ci gaba da bada hadin gwiwa ga jami’an tsaro domin samun ingantaccen tsaro a jihar.

Ya kuma kara da cewa kare rayuka da dukiyoyi wani nauyi ne na hadin gwiwa, saboda haka akwai bukatar dukkan mazauna yankin su bawa jami’an yan sanda hadin kai domin magance matsalar rashin tsaro.

Kwamishinan ya kara da cewan ”An yi kiyasin cewa jihar Nasarawa na daga cikin johohi mafi zaman lafiya a kasar saboda dabarun hadin gwiwa da ake samu daga al’ummomi, da kuma goyon bayan gwamnatin jihar,” in ji shi.

(NAN)

https://www.youtube.com/watch?v=EUt5uzdmQs4

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories