spot_imgspot_img

Ko Kun San Amfanin Yayan Gwanda Ga Lafiyar Dan Adam

Gwanda itaciya ce da yayanta ke dauke da wadataccen sinadarin bitamin C, wanda ke taimakawa wajen kare jiki daga cututtuka samar da collagen, inganta lafiyar fata, Lafiyar gashi, da kuma farce.

Ga Kadan Daga Cikin Amfanin su ga lafiyar Dan Adam

Inganta narkewar abinci Kwayoyin gwanda na ƙunshe da wani sinadarin enzyme mai suna papain wanda ke taimakawa wajen narkar da abinci. shan cokali ɗaya na yayan gwanda bayan cin abinci na taimakawa wajen narkewar abinci da kuma hana kumburin ciki.

Inganta lafiyar hanta Bincike ya nuna cewa yayan gwanda na dauke da antioxidants, wanda ke taimakawa wajen cire sinadarai masu illa a jiki da kuma taimakawa ayyukan hanta a jiki saboda irin sinadaran da ke dauke jikin yayan ,shan ‘ya’yan gwanda cokali guda a ruwa ka iya taimakawa hakan.

 Rage kiba samun ingantaccen fiber a yayan gwanda na taimakawa sosai wajen rage kitse da kuma daidaita sukari a jini.

Nakuda Yayan gwanda na taimakawa matuka ga mace mai ciki a duk lokacin da nakuda ta taso idan ta kwaba garin ta lasa hakan na taimakawa matuka wajen saukaka haihuwa.

Cutar Ulsa Yayan gwanda na da amfani ga mai fama da cutar ulsa idan ya lazamci sha

Ruwan Maniyyi a fannin zamantakewar aure shan garin yayan gwanda da madara na taimakawa sosai wajen karuwar ruwan maniyyi.

Magance Cutar Siga A samu yayan gwanda a busar a dinga sha hakan na taimakawa wajen saukar da cutar siga ga masu fama da ita.

Tsarin Iyali duk da dai babu binciken bincike da ya tabbatar da hakan amma dai da yawa cikin mutane na amfani da shan garin yayan gwanda a ruwan dumi wajen tsarin iyali hakan na taimakawa wajen hana mace daukar ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories