spot_imgspot_img

Kungiyar ASUU Reshen Jami’ar Sa’adu Zungur Ta Janye Yajin Aiki

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Sa’adu Zungur (SAZU), ta dakatar da yajin aikin dindindin da ta fara kimanin makonni biyu da suka gabata.

ASUU ta ayyana yajin aikin ne a ranar 29 ga Nuwamba domin matsawa gwamnan Bauchi lamba kan rashin tsarin fansho da fansar mutuwa ga ma’aikatan SAZU, da biyan kudaden alawus n da kuma wasu hakkokin su da ba a biya ba.

Shugaban ASUU na jami’ar, Kwamared Auwal Nuhu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Kungiyar NLC A Jihar Bauchi Za Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba-ta-gani

Manyan Lakcarori Fiye Da 30 Sun Ajiye Aiki A Jami’ar Jihar Bauchi

Jihar Bauchi Za Ta Fara Biyan Sabon Albashin N70,000 A Nuwamba

Ya ce an cimma matsayar dakatar da yajin aikin ne a wani taron gaggawa da aka gudanar ranar 14 ga Disamba, 2024 a harabar Jami’ar a Yuli, bayan tattaunawa mai ma’ana da kungiyar tayi da gwamnan jihar Bauchi, wanda shi ne Mai Ziyarar Jami’ar.

Kwamared Nuhu ya bayyana cewa ASUU ta rattaba hannu kan wata takardar fahimtar juna (MoU) tare da gwamnatin Bauchi domin magance matsalolin da suka haifar da yajin aikin.

“Wadannan ci gaban sun nuna jajircewar gwamnati wajen bunkasa ilimi a jihar Bauchi. Taron ya yaba wa Gwamna Mohammed kan irin dabarun da ya dauka don magance matsalolin,” in ji sanarwar.

“Saboda wadannan ci gaba, Taron ya yanke shawarar dakatar da yajin aikin nan take,” sanarwar ta kara da cewa.

Kwamared Nuhu ya tabbatar da cewa ASUU za ta ci gaba da sa ido tare da jajircewa don tabbatar da an cika yarjejeniyoyin da aka kulla.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories