Majalisar malaman addinin Musulunci a jihar Bauchi (BSMP) ta yi kakkausar suka tare da nuna adawa a kan yunkurin kafa hedikwatar masarautar Sayawa a garin Tafawa Balewa, su na ma su bayyana hakan a matsayin abinda ya ci karo da zahirin al’adun mazauna yankin.
Shugaban majalisar malaman, Yusuf Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai a garin Bauchi.
Malam Yusuf ya bayyana cewa basa adawa da kafa masarautar Sayawa saboda kundin tsarin mulki ya bada damar hakan, amma ya ce, “ko kadan bamu amince da shawarar gwamnatin jihar Bauchi na yin amfani da garin Tafawa Balewa a matsayin hedikwatar masarautar Sayawa ba.”
A cewar Malam Yusuf, tarihi ya nuna cewa Tafawa Balewa garin Fulani ne tare da bayyana cewa, “akwai sahihan bayanai da alkaluma na tarihi da su ka tabbatar da hakan”.
Malamin ya bayyana cewa hatta kwamitin da gwamnatin jihar Bauchi ta kafa kafin kirkirar masarautar Sayawa ya nuna cewa a kafa hedikwatar masarautar a karamar hukumar Bogoro saboda Tafawa Balewa muhallin Fulani ne.
KARANTA:Â Rashin Girmama Lokaci: Yadda Gwamnan Bauchi Ya Kaskantar Da Sarakuna Da ‘Yan Majalisa
Gwamnatin Bauchi Za Ta Gina Cibiyar Wutar Lantarki Mai Amfani Da Hasken Rana
Yadda Aka Tsinci Jaririn Kwana Daya A Bolar Garin Bauchi
BAUCHI: ‘Yan Sanda Za Su Tono Gawar Wata Yarinya Mai Shekara Biyu Da Ake Zargin An Kashe
“Tsarin siyasa, a duk duniya, bai yarda da rashin adalci ba, bai yarda da karya doka ba, bai yarda gungun wasu mutane su take hakkin wasu ba,” a cewar Malam Yusuf.
Kazalika, ya roki mambobin majalisar dokokin jihar Bauchi su yi aiki bisa ‘gaskiya da adalci’ tunda yanzu batun yanke shawara a kan wurin kafa hedikwatar masarautar Sayawa ya dawo hannun su.
Malam Yusuf ya kara da cewa mayar da hedikwatar masarautar Sayawa zuwa Tafawa Balewa zai kara rura wutar zaman dar-dar da aka dade ana yi tsakanin mabiya mabanbanta addinai a yankin.
“Musulmai mazauna Tafawa Balewa su na kira a yi wa lamarin duba na tsanaki, a kalli lamarin ta fuskar siyasa da zamantakewa, domin tabbatar da gaskiya da adalci,” a cewar sa.
Ya ce majalisar malamai ba zata taba goyon bayan kafa hedikwatar masarautar Sayawa a Tafawa Balewa ba, saboda yin hakan tamkar yi wa ‘yan asalin wurin kwacen kasa da albarkatu ne.



