Wasu matasa da ake zargin ‘yan Sara-Suka ne sun kona ajujuwan Makarantar Firamare ta Kandahar, da ke Bauchi, bayan wani rikici da Kwamitin Tsaro na unguwar.
Matasan sun ƙona makarantar ne bayan sun ƙone ofishin Kwamitin Tsaron, wanda yake kusa da makarantar.
Mai magana da yawun Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Bauchi (SUBEB), Mohammed Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga WikkiTimes ranar Asabar.
KARANTA WANNAN: KALARE: Yadda Yan Sanda Suka Kama Masu Kwacen Waya A Gombe
Majalisar Malaman Bauchi Ta Yi Watsi Da Yunkurin Kafa Daular ‘SAYAWA’ A Tafawa-Balewa
Dubu Ta Cika : Ƴan Sanda Sun Kama Masu Fashi, Sata A Bauchi
“Ƴan sara-sukan sun ƙona makarantar tare da ofishin jami’an tsaro kwana ɗaya bayan rahoton rikicin.
“Makarantar an gina ta ne domin amfanin al’ummar yankin. Duk da haka, sun ƙona wani bangaren ɗakunan karatun.
“Abin takaici ne ganin wannan ɗabi’ar rashin imani a lokacin da gwamnatin jiha ke ci gaba da ƙoƙarin gina sabbin makarantu da gyara tsofaffin gine-ginen domin samar da yanayi mai kyau ga koyarwa da koyo,” inji shi.
Abdullahi ya bayyana cewa matasan suna ci gaba da aikata barna a makarantu ta hanyar sata da wasu munanan halaye na laifi.
“A wani lamari makamancin wannan a bara, wasu matasa a Bakaro sun ƙona wata makaranta jim kaɗan bayan gwamnati ta fara rushewa da gyaran makarantar.
“Matasan sun nemi a basu tsofaffin karafunan rufi da aka cire daga tsohon ginin, amma an hana su. Wannan ya fusata su har suka ƙone makarantar.
Ya ƙara da cewa ana ƙoƙarin neman waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban shari’a.



