Makarantun Firramare da kananan Sakandire a fadin jihar Bauchi su na fuskantar barazanar durkushewa saboda sakaci da gazawar gwamnati da hukumomi na inganta makarantun da daukar kwararrun Malamai. Sakamakon binciken jaridar WikkiTimes ya tono irin halin lalacewar da irin wadannan Makarantu ke ciki a yayin da gwamnati ta ke cigaba da nuna halin ko in kula.
A Maraban Liman Katagum, wata unguwa da ke gefen garin Bauchi, wakilin jaridar WikkiTimes ya ga wani dalibi, Musa Ahmad, mai shekaru 14, a yayin da ya ke zaune yana rubutu a dandamalin kasa a cikin aji a karamar sakandire (GJSS) Maraba.
A cikin ajin akwai Malami (an boye sunan sa saboda dalilan sirri) ya na kokarin yin bayanin darasin lissafi wanda bisa dukkan alama shi kan sa bashi da kyakyawar fahimtar darasin. Akwai alamun rudewa a fuskar Musa saboda ya gaza fahimtar Malamin duk da ya mayar da hankali domin ya gane darasin.
Daga baya wakilin WikkiTimes ya gano cewa an dauki Malamin aiki ne domin ya koyar da darasin zamantakewa (Social Studies) amma aka mayar da shi na lissafi saboda babu mamalamin lissafi a makarantar.
“Ba lissafi na karanta ba, amma yanzu shi nake koyarwa. Ba ni da wani zabi, Daliban su na bukatar Malami kuma babu kowa bayan ni,” a cewar Malamin.
Malamin, wanda shi kadai ne a Makaranta mai dalibai fiye da 300, kyakyawan misali ne na irin halin karancin kwararrun Malamai da makarantun jihar Bauchi ke ciki.
Wannan matasalar ta fi zama gama gari a makarantun Firamare da kananan makarantun Sakandire. Inda ake bawa malamai darasin Lissafi da Turanci domin su koyar a yayin da ba bangaren karatun su ba ne.
“Maganar gaskiya shine muna bukatar karin Malamai. A yanzu haka, ba mu da Malamin karatun ilimin noma. Wasu lokutan Malamin Hausa ne ya ke taimakawa, amma duk da haka dai bai wadatar ba,” kamar yadda Malamin ya bayyana cikin alamun gajiyawa.
A cewar Malamin, a kalla makarantar tana bukatar Malamai 25 domin gudanar da aikin koyo da koyarwa yadda ya kamata amma Malamai 9 ne kacal a makarantar, kamar yadda ya nuna a cikin wani tsohon littafi da ke zaman rijistar Malamai, wanda Malamin ya ce su ne suka siya da dan kudin aljihun su.

Kazalika, Malamin ya bayyana takaicinsa a kan yadda ake nuna wariya yayin daukar aiki wanda hakan ke kara haifar da matsala. “Wasu daga cikin Malaman ‘ya’yan manya ne da basa zuwa aiki sai sun ga dama. Wadan su kuma, za su iya aikin, amma su na da nisa, a saboda haka ba zasu iya dawainiyar biyan kudin mota kwana biyar a sati ba,” a cewar sa.
Har ila yau, Malamin ya bayyana yadda ake daukar ma su iya kwalin shaidar karatun koyar da addini (Islamic Studies). “Muna da Malaman Islamic guda hudu wadanda ba zasu iya koyar da wani darasin ba duk da muna matsa musu sai sun gwada,” kamar yadda Malamin ya bayyana.
Sannan ya kara da cewa; “ko a unguwar nan akwai ma su takardar shaidar kwarewa a koyarwa (NCE) amma suna nan a zaune a gida, babu aiki, a yayin da ake fama da karancin Malamai ma su kwarewa a ajujuwa”.
Matsalar Ba Iya Nan Ta Tsaya Ba
Kimanin nisan kilomita 10 daga makarantar GJSS Maraba, akwai wata makarantar makiyaya da ta shafe shekaru 16, amma a tsawon fiye da shekara 10, Malami daya ne a makarantar mai dalibai fiye da 300. Shi ma Malamin ya rasu a farkon shekarar 2024, lamarin da ya bar yara a makarantar babu Malami.
Haka matsalar ta ke, ba ta canja zabi ba, a karamar hukumar Dass. Wani Malami a makarantar karamar sakandire (GJSS), Husaini Wandi, ya bayyana yadda karancin malamai a makarantar ya nakasta koyo da koyarwa.
“Mu na bukatar karin Malamai. Daga cikin Malamai 12 da mu ke da su, guda hudu Malaman Islamic ne, sai wasu hudun Malaman ‘Basic Science’, amma babu Malamin lissafi wanda ya ke dole ga duk dalibai.
“Matasa ‘yan bautar kasa ne ke koyar da darasin Turanci, sannan akwai Malamin ilimin motsa jiki (PHE) guda daya. A hakan, alhakin mu ne mu kula da koyar da dalibai fiye da 200. Tun shekarar 2014 rabon da gwamnati ta dauki Malaman Makaranta”, a cewar sa.
A karon farko da wakilin WikkiTimes Hausa ya kai ziyara a ranar 30 ga watan Oktoba, a rufe ya samu makarantar. Bayan ya kira daya daga cikin Malaman Makarantar sai ya sanar da shi cewa sun tafi wurin tantance ma’aikata a Bauchi.

Da wakilin mu ya kara komawa a ranar 5 ga watan Nuwamba, Malamai guda uku kacal ya samu. Malaman sun bayyana cewa da kudin aljihun su da tallafin iyayen yara, a wasu lokutan, su ke siyan kayan aiki kamar irin su Alli da Rijistar dalibai.
Bayanan da WikkiTimes ta tattaro sun nuna cewa ba bakon abu ba ne a samu Malami daya yana koyar da darussa fiye da daya a sati. Lamarin da ya haifar da dusashewar nagartar ilimi a makarantun gwamnati da ‘ya’yan talakawa da marasa galihu su ke halarta.
Makarantu Da Yawa A Rufe
Kamar yadda lamarin ya ke a makarantun JSS Wandi da Dabardak a karamar hukumar Dass, haka ya ke a makarantar JSS Ajili a karamar hukumar Misau, inda wakilin mu ya iske babu Malamai, babu dalibai a ranar 6 ga watan Nuwamba da ya kai ziyara.
“Babu wanda ya zo, ku san haka lamarin ya ke koda yaushe,” a cewar Malamin wata Makarantar Firamare kusa da JSS Ajili. Ya kara da cewa, “malamai uku ne kacal a makarantar, bisa alama kuma sun gaji da zuwa.”
A Giade ma haka mataslar ta ke babu canji. Ba a bude makarantar Firamare ta garin Zankam ba a ranar 17 ga watan Oktoba, babu Malami a yayin da wakilin mu ya kai ziyara Makarantar ranar 17 ga watan Oktoba.

Kafin hakan, shugaban makarantar, Alhaji Haruna, ya taba korafin cewa akwai Malamai biyu ne kacal a makarantar.
A kauyen Abbakorawa ma haka matslar ta ke. Malamai biyu ne kacal a makarantar, shugaban makarantar daga wani kauyen ya ke zuwa, a saboda haka ba kullum ya ke zuwa ba kuma Malamin Arabic ne.
“Su dama daliban sun daina zuwa saboda rashin zuwan Malamai,” a cewar wani dattijo a kauyen, Malam Muhammadu, wanda ya kara da cewa, “idan sun zo ba su samu Malamai ba, sai su tafi ba lallai kuma su sake dawowa a cikin satin ba.”
“Abin yana min ciwo, ganin yadda yaran mu su ke zaune ba tare da zuwa makaranta ba, amma babu abin da mutum zai iya yi,” a cewar sa.
Cutarwa Ga Dalibai
Kamar Musa a Mararaba, Aisha Sagir, daliba mai shekaru 16 a Misau, ta koka cewa, “kamar shi ma Malamin bai gama fahimtar wasu darussan ba. Haka wasu lokutan zai bar mu ba tare da mun fahimci darasin ba, mu kuma bamu san ya abin ya ke ba.”
Bincike ya nuna cewa jihar Bauci ta dade tana fama da matsalar karancin Malamai musamman a kauyuka.
A shekarar 2023, gwamnatin jihar Bauchi ta amince cewa akwai makarantu 79 da suke da Malami daya a karamar hukumar Misau. Amma, duk da hakan, jami’in gwamnati ya bayyana cewa a hakan ma karamar hukumar ta fi wasu kananan hukumomin da yawa idan aka kwatan ta.
“A hakan ma Misau ta fi wasu kananan hukumomin a jihar Bauchi. Ka je wasu kananan hukumomin ka gani,” a cewar Korijo Usman, darektan makarantu a hukumar kula da ilimin bai daya (SUBEB) a jihar Bauchi, Korijo Usman.
Yadda Matsalar Ta Shafi Malamai
Dole zai kasance akwai nakasu idan aka bukaci Malami ya koyar da darasin da shi kan sa bai fahimta ba, tun farko ma zai fuskanci kalubale wajen tsara yadda zai koyar da darasin, kamar yadda wata malama, Fatima Muhammed, a makarantar karamar sakandire a Ningi, ta bayyana.
“An dauke ni aiki ne domin na koyar da ilimin zamantakewa amma yanzu alhakina ne na koyar da Turanci da Ilimin noma a wasu lokutan. Kullum ba na iya kwanciya da wuri saboda kokarin na karanta litattafai domin fahimtar darasin da zan koyar da tsara yadda zan koyar da shi domin yara su fahimta. Aiki ne mai matukar wahala,” a cewar ta.
Irin wannan tulin aikin da rashin albashi mai kyau su ne su ke saka Malaman makaranta irin Fatima yi wa kan su tambayar anya kuwa ba su yi rashin sa’ar aiki ba.
Karsashin ta na son koyarwa kullum sai kara dusashewa ya ke yi saboda irin kalubalen da ta ke fuskanta. “Ina son koyarwa, amma yanzu, duk na ji na gaji, ina jin tamkar ina cin dunduniyar dalibai na.”
Duk da gwamnati ta aminta a kan cewa akwai kalubale a bangaren ilimi kuma akwai bukatar yin gyara, har yanzu babu wani mataki da ta dauka, ta rufe ido tare da yin burus da matsalar da ba zata haifar da gobe mai kyau ba.
Wani mai ruwa da tsaki a bangaren ilimi kuma tsohon shugaban sashen harkokin makarantu, Jibrin Saleh, ya bayyana lamarin a matsayin barazana ga rayuwar yara, manyan gobe.
Jibrin, wanda ya yi aiki a karamar hukumar Dass kafin ya yi ritaya, ya bayyana gazawar gwamnati wajen daukan Malamai a matsayin babbar matsala.
“Lokacin da aka dawo da ni Dass da aiki, a shekarar 2016, mu na da Malamai ku san 800. Amma, a shekarar 2022 da na bar aiki, adadin Malaman ya ragu zuwa kasa da 500. Malamai su na yin ritaya, sannan wasu su na mutuwa, duk shekara ba tare da maye gurbin su ba” a cewar sa.
A cewar Jibrin, wannan ita ce babbar matsalar da ke barazanar kawo durkushewar harkokin ilimi a jihar.
‘Yan Sa Kai Sun Kawo Agaji
Saboda karancin Malamai, matasan da su ka kammala karatun digiri da kwalejin horon Malamai sun kawo agaji domin cike gurbin karancin Malamai a wuraren da su ke zaune.
Malamai ne su ke hada dan wani abu domin a bawa irin wadannan matasa ‘yan sa kai domin karfafa mu su gwuiwa. A wasu lokutan ma ba a basu komai.
“Akwai wadanda daga cikinsu ake bawa N3,000 duk wata amma a haka su ke yin aikin saboda kishi da son taimakawa al’ummar su,” a cewar Jibrin.
Jibrin ya bayyana cewa shi kan sa a gidan sa yana da yara biyu da su ka kammala manyan makarantu amma ba a dauke su aiki ba duk da sun samu horon koyarwa.
Aliyu Usman Tilde, tsohon kwamishinan ilimi a jihar Bauchi, ya amince cewa akwai bukatar a dauki kwararrun Malamai.
Kazalika, ya bayyana rashin daidaito a bangaren kwarewar Malaman da ake da su a matsayin wata babbar matsala a bangaren ilimin jihar.
A shekarar 2023, Abdullahi Abubakar, wani kwararre mai aiki da USAID a karkashin shirin “LEARN to Read” ya bayyana cewa bangaren ilimi a Bauchi yana cikin mawuyacin hali a yayin da makarantun gwamnati 207 a jihar babu Malami ko daya.
Rahotanni sun sha nuna kwazon daliban jihar Bauchi a cikin mafi muni a jarrabawoyin kammala makarantar sakandire kamar su WAEC, NECO, NABTEB da NBAIS.
Iyayen Yara Sun Koka
Iyayen yara sun nuna damuwar su. Salamatu Adamu, wata uwa mai yara hudu a Gamawa, ta bayyana takaicin ta a kan tabarbarewar nagartar ilimin da yaran ta su ke samu.
“Idan na tura yara na makaranta sai su dawo koda yaushe su ce min ba su gane darasin da aka yi ba, duk lokacin da mu ka tambaye su amsar su kenan. Ta yaya yara zasu yi nasara idan Malamansu ba su san yadda za su koyar da su ba?” Salamatu ta tambaya.
A cewar Salamatu, karancin Malamai ya hana yara samun damar koyo daga kwararru da suke da gogewa.
“Shugabannin mu basu damu da bangaren ilimi ba. Kullum sai maganar gyara kawai su ke yi a baki, amma ba za a ga aikin a kasa ba,” a cewar ta.
Shekaru da yawa sun shude gwamnatin jihar Bauchi tana daukan alkawarin kaddamar da tsarin daukan ma’aikata domin cike gurbin karancin Malaman makaranta.
Mohammed Abdullahi, mai magana da yawun hukumar ilimin bai daya (SUBEB) a Bauchi, ya ce su na sane da kalubalen.

A cewar Mohammed gwamnatin jiha ta bayar da izinin daukan karin Malaman makaranta ”amma kuma wasu matakai da ka’idojin aikin gwamnati sun kawo tsaiko na wucin gadi”, kamar yadda ya bayyana ba tare da fadin wadanne irin matakai da ka’idoji ba ne.
Sai dai, ya bayyana cewa kafa sabuwar hukumar kula da malamai (TSC) zai kawo karshen tsaikon da ake samu a bangaren daukan karin Malaman, wanda ya bayyana cewa ”na san su na aiki tukuru domin ganin hakan ta tabbata.”
A cewar Mohammed, tun 2014 rabon da gwamnati ta dauki sabbin Malaman makaranta amma sun dauki mutum 1,000 mata da UNICEF ta bawa horon koyarwa.



