spot_imgspot_img

Gwamnan Jihar Bauchi Ya Nada Sabon SSG Da PPS

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya amince da nadin sabon sakataren gwamnati (SSG) da kuma babban sakatare na musamman (PPS) biyo bayan ajiye aiki da tsohon SSG, Kashim Ibrahim, ya yi.

Alhaji Aminu Hammayo, kwamishinan kasafin kudi na jihar Bauchi, shi ne wanda gwamna Bala ya nada a matsayin sabon SSG a yayin da ya nada Alhaji Hashimu Kumbala a matsayin sabon PPS.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa Gwamna na musamman a harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya rabawa manema labarai da safiyar ranar Juma’a a garin Bauchi.

Sanarwar ta bayyana cewa: “Alhaji Aminu Hammayo, gogaggen ma’aikacin gwamnati ne da ya yi aiki a wurare da dama inda ya bayar da gudunmawar sa wajen hidimtawa jiha. An san shi a matsayin mutum mai kwazo, gaskiya, da rikon amana.

KARANTA: Gwamnatin Jihar Bauchi ta Fara Gyaran Asibitin Dabar Baga, Bayan Rahoton WikkiTime

Gwamnatin Bauchi Za Ta Gina Cibiyar Wutar Lantarki Mai Amfani Da Hasken Rana

BAUCHI: An Kama Wata Mata Mai Shekara 40 Da Matasa 4 Da Laifin Fashi Da Makami

Rashin Girmama Lokaci: Yadda Gwamnan Bauchi Ya Kaskantar Da Sarakuna Da ‘Yan Majalisa

“A baya ya taba rike mukamin SSG kafin daga baya a nada shi a matsayin kwamishinan kasafin kudi. Yanzu kuma an sake mayar da shi kan tsohon mukamin sa,” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa; “Alhaji Hashimu Kumbala, kwararren ma’aikaci, zai kasance babban sakatare na musamman ga mai girma Gwamna. A sabon mukamin sa, zai ke bawa Gwamna shawarwari a kan gudanar da harkokin aikin ofis tare da tabbatar da samun sadarwa da tsara aiyukan cikin gwamnati. Tsohon babban sakataren Gwamnati ne, sannan, kafin nadinsa a wannan sabon mukami, ya na daga cikin ma su bawa Gwamna shawara.”

A baya, WikkiTimes ta wallafa rahoton cewa sakataren gwamnatin jihar Bauchi ya yi murabus. Sai dai, wata majiya a fadar gwamnatin jihar ta bayyana cewa tilasta masa ajiye aikin aka yi.

Ya zuwa yanzu babu wani dalili na zahiri a kan abin da ya faru da tsohon SSG, wanda ake yi wa ganin tamkar ‘sarkin fadar gwamna Bala’, har ta kai ga an sauya shi.

Sanarwar ta bayyana cewa za a rantsar da wadan da aka nada a ranar Juma’a, 27 ga watan Disamba, a gidan gwamnatin jihar Bauchi da misalin karfe 12:00 na rana.

Naziru Taura
Naziru Taurahttp://wikkitimes.com/hausa
Naziru Taura is a dedicated teacher, Hausa blogger, freelancer, and translator with a passion for education, information dissemination, and purposeful leadership. He specializes in crafting compelling stories in both English and Hausa, focusing on the Sustainable Development Goals (SDGs) and amplifying the voices of marginalized and underreported communities. Through his work, Naziru offers hope, advocates for justice, and drives meaningful conversations on societal progress. With over a decade of experience, Naziru has produced numerous impactful stories, shedding light on business and economic empowerment opportunities. His investigative work has also uncovered cases of corruption, abuse of power, and the mismanagement of public funds, showcasing his commitment to accountability and transparency.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories