Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da bayar da aiki kai tsaye ga dalibai ‘yan asalin jihar da suka kammala karatun digiri na biyu a bangaren fasaha, likitanci, magunguna, da sauran karatun lafiya a kasar India.
Tun farko, gwamnatin jihar Kano ce ta dauki nauyin tura daliban kasar India domin karo karatun digiri na biyu bayan kammala karatun digiri na farko a gida Nigeria.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin-Tofa, shine ya sanar da hakan ranar Asabar a Kano.
Tawagar gwamnatin jihar Kano, a karkashin jagorancin mataimakin gwamna, Aminu Abdulsalam, da kwamishinoni da sauran manyan kusoshin gwamnati, su ne suka tarbi Daliban a filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano bayan dawowar su.
A cewar Dawakin-Tofa, wadanda suka ci moriyar tallafin karatun da aiki kyauta sun yi karatu a jami’o’in kasar India da dama, amma 150 daga cikin su sun kammala karatun su ne a jami’ar Sharda.
Dawakin-Tofa ya bayyana cewa Gwamna Abba ya yabawa daliban bisa kokari da jajircewar da suka nuna a makarantun da suka halarta.
KARANTA:Â Kano: Abba Ya Mika Sunayen Mutum 6 Da Zai Nada A Matsayin Sabin Kwamishinoni
Sakaci Da Aiki: Abba Ya Kori Dan Kwangilar Aikin Gina Titi A Kano
Garba Kwanwkaso Ya Maka Abba Gida- Gida A Kotu Kan Rikicin Fili
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata liyafar karramawa da ya shiryawa daliban, inda ya bayyana hakan a matsayin daya daga cikin manyan nasarorin gwamnatin sa na gina dan adam.
Abba ya bayyana cewa bawa matasan aiki ya sake tabbatar da kokarin gwamnatinsa na warware matsalar karancin kwararrun ma’aikatan lafiya da bangaren aiyukan raya kasa.
“Wannan abu da mu ka yi yana daga cikin kudirin mu na tallafawa matasa domin su gina Kano da muke fatan gani a gobe.
“Muna ma su alfahari da nasarorin da ku ka samu, sannan mu na da karfin gwuiwar cewa za ku bayar da gudummawa wajen dorewar manufar mu ta kawo cigaba,” a cewar Abba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.



