spot_imgspot_img

An Kama Matar Da Ke Yiwa Bello Turji Safarar Alburusai A Zamfara

Dakarun rundunar soji ta ‘Fansan Yamma’ ta kama wata mata, Shamsiyya Ahadu, mai shekaru 25, bisa zargin ta yin safarar alburusai ga ‘yan ta’adda.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da mai kula da yada labarai na rundunar, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi, ya fitar ranar Lahadi a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

A cewar jawabin, an kama Shamsiyya ne tare da wani Dan-acaba, abokin aikin ta, mai suna Ahmed Husaini, a yankin garin Badarawa da ke karkashin karamar hukumar Shinkafi.

An same ta da alburusai 764 na musamman (7.62mm) da kuma wasu kwanson alburusai guda 6 a hanyar su ta zuwa kai su sansanin jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji.

KARANTA: Mutane 12 Sun Mutu Bayan Tashin Bam A Jihar Zamfara

Yan Bindiga Sun Kona Gonaki Sun Sace Mutane A Zamfara

Yan Sanda Sun Ceto Fasinjoji 14 daga Hannun Yan Bindiga A Katsina

Nan Ba Da Jimawa Ba Zamu Damƙo Bello Turji – CD

“An samu nasarar kama ta bayan tattara bayanan sirri a kan yadda ake kai wa ‘yan bindiga kayayyaki ta hanyar da ta tashi daga Kware zuwa Badara a karamar hukumar shinkafi.

“Bayan samun bayanan ne sai dakarun mu na rundunar Fansan Yamma su ka saka shinge a kan hanyar, lamarin da ya kai ga an samu nasarar cafke wadanda ake zargi.

“Yanzu haka wadanda ake zargin su na hannun hukumomin da su ka dace kuma ana gudanar da bincike,” a cewar jawabin.

Rundunar soji ta kara jaddada niyyar ta na tarwatsa duk wani sansani da hadakar ‘yan ta’adda da ma su yi musu safarar makamai.

A karshe, rundunar sojin ta yi kira ga jama’a da su cigaba da bawa jami’an tsaro sahihan bayanai da za su kai ga samun nasarar kama ma su taimakawa ‘yan ta’adda.

Naziru Taura
Naziru Taurahttp://wikkitimes.com/hausa
Naziru Taura is a dedicated teacher, Hausa blogger, freelancer, and translator with a passion for education, information dissemination, and purposeful leadership. He specializes in crafting compelling stories in both English and Hausa, focusing on the Sustainable Development Goals (SDGs) and amplifying the voices of marginalized and underreported communities. Through his work, Naziru offers hope, advocates for justice, and drives meaningful conversations on societal progress. With over a decade of experience, Naziru has produced numerous impactful stories, shedding light on business and economic empowerment opportunities. His investigative work has also uncovered cases of corruption, abuse of power, and the mismanagement of public funds, showcasing his commitment to accountability and transparency.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories