spot_imgspot_img

Gwamnatin Yobe Ta Samar Da Sabon Matsuguni Ga Mutanen Da Ambaliya Ta Shafa

Gwamnatin jihar Yobe ta fara mayar da mutanen da ambaliyar ruwan sama ta lalatawa gidaje zuwa sabon matsugunin da aka samar mu su.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, shine da kan sa ya kaddamar da fara yin hijirar mutanen Kirikasamma da ke yankin karamar hukumar Geidam.

Sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Yobe (SEMA), Muhammad Goje, shine ya sanar da hakan a shafin sa na dandalin sada zumunta, Facebook, yayin da ya ke jaddada manufar gwamnati na kawo karshen matsalar ambaliyar ruwan sama da mazauna yankin ke fuskatanta.

“Tsawon shekaru kenan da mutanen garin Kirikasamma fiye da 500 su ke zaman wucin gadi a garin Geidam bayan ambaliyar ruwan sama ta yi sanadiyyar rushewar gidajen su 114. Yawancinsu su na zaune ne a rukunin gidajen Mai Mala,” a cewar sa.

A cewar Muhammad, gwamnati ta gudanar da bincike mai zurfi, wanda ya hada har da na tsaro, kafin fara rabawa wadanda abin ya shafa sabbin matsuguni da zasu zauna tare da iyalansu domin sake gina sabuwar rayuwa.

KARANTA: YOBE: ‘Yan Sanda Sun Kama Wata Mata Mai Shekaru 54 Da Alburusai 350

Jigawa Za Ta Ci Moriyar Shirin Bunkasa Noma Da Bankin Duniya Ya Ware $500m

Ƴan Sanda Sun Cafke Wani Magidanci Bisa Zargin Kisan Matarsa a Yobe

Fitinannen Mai Garkuwa Da Mutane Ya Fada Komar ‘Yan Sanda A Yobe

Ya bayyana cewa an fara shirin mayar da su sabon matsugunin a hukumance ta hanyar fara raba mu su kudi da kayan amfani wanda hukumar SEMA ta jagoranta.

Ya kara da cewa gwamnatin jiha ta ware fili mai girman hekta 8.53 a matsayin muhalli da wurin noma ga kowanne Magidanci tare da bayyana cewa an basu wuraren ne kyauta da sharadin mutum ba zai bayar ga wani ba.

Muhammadu ya ce ana cigaba da samar da sauran kayan more rayuwa da suka hada da ruwa mai tsafa, makaranta, da asibiti domin moriyar mutanen.

Babban sakataren ya tabbatar da cewa an samu hadin kai da goyon bayan ma su ruwa da tsaki da suka hada da karamar hukumar Geidam, Ma su rike da sarautar gargajiya, wakilan sarkin Ngazargamu, da jami’an tsaro kafin fara sauyawa mutanen matsuguni.

Naziru Taura
Naziru Taurahttp://wikkitimes.com/hausa
Naziru Taura is a dedicated teacher, Hausa blogger, freelancer, and translator with a passion for education, information dissemination, and purposeful leadership. He specializes in crafting compelling stories in both English and Hausa, focusing on the Sustainable Development Goals (SDGs) and amplifying the voices of marginalized and underreported communities. Through his work, Naziru offers hope, advocates for justice, and drives meaningful conversations on societal progress. With over a decade of experience, Naziru has produced numerous impactful stories, shedding light on business and economic empowerment opportunities. His investigative work has also uncovered cases of corruption, abuse of power, and the mismanagement of public funds, showcasing his commitment to accountability and transparency.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories