spot_imgspot_img

Jigawa: Gidaje 4 Sun Kone Kurmus Bayan Mota Ta Kwace Daga Hannun Dan Koyon Direba Ta Shiga Unguwa A Dutse

Rundunar ‘yan sanda a birnin Dutse, jihar Jigawa, ta tabbatar da konewar wasu gidaje hudu kurmus a yayin da wata mata da yaran ta suka tsira da kyar bayan wani direba da ake zargin a buge ya ke ya kutsa kai da mota cikin wani gida.

A cewar rundunar ‘yan sandan, lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi yayin da wata mota, da ake zargin direban ta ya kwankwadi barasa kafin ya hau tuki, ta ture katangar wani gida da wata mata da yaran ta su ke ciki su na bacci.

Shiisu Lawal Adam, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya ce ya yi sanadiyyar rushewar gidan tare da tashin gobarar da ta shafi karin wasu makwabtan gidaje guda uku.

A cewar sa, da kyar jama’ar unguwa da hadin gwuiwar jami’an tsaro su ka samu nasarar shawo kan gobarar. Ya kara da cewa binciken farko da su ka fara gudanarwa ya gano cewa direban motar ba a cikin hayyacinsa ya ke ba.

KARANTA: JIGAWA: FG Ta Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwa A Dutse A Kan Biliyan N59.4

Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe N117m Domin Samar Da Cibiyar CNG A Dutse

Jigawa: An gano Ma’aikatan Bogi 6,348 Da AKe Kashewa 3.7bn A Matsayin Albashi

Jigawa: Ma’aikatar Muhalli Da Hadin Gwuiwar Kungiyar GAFF Sun Yi Taron Ranar Kiyaye Gurbatar Muhalli

“A Sakamakon hakan, da motar da gidan duk sun kone kurmus, sannan kuma lamarin ya shafi sauran wasu makwabtan gidaje guda uku, wadanda su ma su ka kone kurmus,” a cewar Shiisu.

Ya kara da cewa duk da ba a samu asarar rai ba, an samu nasarar ceton matar tare da yaran ta, amma an samu asarar dukiya ta miliyoyin Naira.

“Duk da cewa, ba a samu asarar rai ba. Binciken da mu ka fara gudanarwa ya gano cewa mai motar sunan sa Muhammad Galadima wanda shi ne da gangan ya bawa Abdullahi Abubakar Sadiq makulin motar, wanda shi kuma ya tabbatar mana da cewa bai iya tuki ba”, kamar yadda Shiisu ya bayyana.

Naziru Taura
Naziru Taurahttp://wikkitimes.com/hausa
Naziru Taura is a dedicated teacher, Hausa blogger, freelancer, and translator with a passion for education, information dissemination, and purposeful leadership. He specializes in crafting compelling stories in both English and Hausa, focusing on the Sustainable Development Goals (SDGs) and amplifying the voices of marginalized and underreported communities. Through his work, Naziru offers hope, advocates for justice, and drives meaningful conversations on societal progress. With over a decade of experience, Naziru has produced numerous impactful stories, shedding light on business and economic empowerment opportunities. His investigative work has also uncovered cases of corruption, abuse of power, and the mismanagement of public funds, showcasing his commitment to accountability and transparency.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories