spot_imgspot_img

Jihar Jigawa Ta Saki Biliyan N1.5 Domin Sallamar Ma’aikatan Da Su Ka Yi Ritaya

Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da sakin kudi, biliyan N1.5, domin fara biyan bashin hakkokin ma’aikatan jihar da su ka yi ritaya.

Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’ada, Sagir Musa, shi ne ya sanar da hakan ta cikin wani jawabi da ya fitar ranar Talata a garin Dutse.

Sagir ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta jiha ta amince da sakin kudin ne yayin zaman ta a ranar Talata.

Ya kara da cewa sakin kudin wata alama ce da ke kara nuni a kan manufar gwamnatin Jigawa a karkashin jagorancin gwamnan jihar, Umar Namadi Danmodi, na inganta walwalar ma’aikatan da su ka yi ritaya tare da biyan su hakkokin su a kan lokaci.

KARANTA: Jigawa: Gidaje 4 Sun Kone Kurmus Bayan Mota Ta Kwace Daga Hannun Dan Koyon Direba Ta Shiga Unguwa A Dutse

JIGAWA: FG Ta Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwa A Dutse A Kan Biliyan N59.4

Jigawa: An gano Ma’aikatan Bogi 6,348 Da AKe Kashewa 3.7bn A Matsayin Albashi

Kwamishinan ya ce za a saki kudin zuwa hukumar kula harkokin fansho wacce a karshe za ta tura kudin zuwa asusun tsofin ma’aikatan da su ke bin gwamnati bashin hakkin sallama kamar yadda ofishin shugaban ma’aikatan jiha ya tantance ya kuma gabatar yayin zaman su na ranar Talata.

A cewar sa, Gwamnan jihar Jigawa ya jaddada kudirin sa na inganta walwala da nutsuwar ma’aikata, hatta a lokacin da su ka yi ritaya. (NAN).

Naziru Taura
Naziru Taurahttp://wikkitimes.com/hausa
Naziru Taura is a dedicated teacher, Hausa blogger, freelancer, and translator with a passion for education, information dissemination, and purposeful leadership. He specializes in crafting compelling stories in both English and Hausa, focusing on the Sustainable Development Goals (SDGs) and amplifying the voices of marginalized and underreported communities. Through his work, Naziru offers hope, advocates for justice, and drives meaningful conversations on societal progress. With over a decade of experience, Naziru has produced numerous impactful stories, shedding light on business and economic empowerment opportunities. His investigative work has also uncovered cases of corruption, abuse of power, and the mismanagement of public funds, showcasing his commitment to accountability and transparency.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories