spot_imgspot_img

Banyi Barazana Ga Shugaban Kasa ba – Gwamnan Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya musanta yin barazana ga Shugaban Ƙasa BolaAhmedTinubu, yana mai cewa kalamansa an ɗauke su a matsayin barazana, amma yana girmama fadar shugaban ƙasa.

Gwamnan ya sanar da hakane a cikin wata takarda mai shafi biyar da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar.

Ya bayyana cewa duk da rashin fahimtar da aka samu dangane da shirin sake fasalin haraji, yana nan daram kan goyon bayan haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya don magance dukkan matsalolin ƙasa, ciki har da dokar sake fasalin haraji don ci gaban ƙasa gaba ɗaya.

KARANTA WANNAN: 

Ka Dakata Da Sake Fasalin Haraji- Gwamnan Bauchi Ga Tinubu

DSS Sun Fara Binciken Sanatan Bauchi A Kan Biyawa Dan Bindigar Zamfara Aikin Hajji

Gwamnonin PDP Sun Buƙaci Gwamnatin Tinubu Da Ta Magance Tsadar Abinci

Ya ce ra’ayin Gwamna Bala Mohammed kan sake fasalin haraji ya dace da na wasu gwamnonin APC da suka gargadi gwamnati kan aiwatar da wannan shirin a yanayinsa na yanzu.

A cewarsa, yana kama da yunƙurin cin zarafi da rashin adalci ga gwamnatin tarayya wajen ware gwamna Bala Mohammed akan wannan batu.

Takardar ta ƙalubalanci fadar shugaban ƙasa cewa yana da kyau tun da gwamnatin tarayya da gaske tana son sake fasalin haraji na haɗin gwiwa, wanda dole sai ya samu amincewar rukunin masu ruwa da tsaki daban-daban a ƙasar, ya kamata ta gabatar da tsarinsa don tattaunawa kafin a miƙa shi zuwa Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories