Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton cewa mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kashe manoma fiye da 40 a wani sabon hari da su ka kai kauyen Kayakura a yankin karamar Kukawa a jihar Borno.
Lamarin, wanda ya yi sanadin raunata wasu manoman ma su yawa, ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Lahadi.
Mazauna yankin sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa mayakan sun kai harin ne a mazabar Doron Baga, inda su ka bude wuta a kan jama’a.
“Maganar da mu ke yi, yanzu haka ba a san inda mutane da yawa su ke ba, sannan sun kashe manoma fiye da 40 da su ka gujewa harin ‘yan kungiyar Boko Haram daga karamar hukumar Gwoza,” kamar yadda wata majiya ta shaidawa Daily Trust.
KARANTA: Borno: An Tsare Shugaban Jam’iyyar NNPP Saboda Sukar Gwamna Zulum
Dakarun MNJTF Sun Dakile Harin ISWAP A Jihar Borno
Gwamnatin Jihar Borno Ta Wanke Mutane 500 Da Ake Zargi Ƴan Boki Haram Ne
Sabon harin ya faru ne bayan kwana daya da kai wani hari a garin Chibok, kudancin jihar Borno, inda mayakan su ka kashe mutane biyu tare da kone wata Coci.
An samu mabanbantan rahotanni a kan adadin mutanen da su ka mutu. Wata majiyar jami’an tsaro ta sanar da cewa mutane 30 ne mayakan su ka hallaka.
“Mutane 30 sun rasa rayukan su sakamakon harin da aka kai wa Manoma a yankin Doron Baga,” kamar yadda majiyar jami’an tsaro ta sanar da Daily Trust.
Kokarin Daily Trust na jin ta bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Kenneth Daso, bai samu ba saboda wayar sa ba ta shiga a lokacin da aka kira shi.



