A kokarinsa na karfafa dangantaka tsakanin sarakunan, Sarkin Ningi, Alhaji Haruna Yunusa Danyaya III, ya fara wata ziyara ta sada zumunci zuwa manyan sarakunan gargajiya a yankin Arewa Maso Gabas.
Bisa al’adar gargajiya, sabbin sarakuna bayan nadinsu daga gwamnatocin jihohi, sukan kai ziyara ga sauran sarakuna don karfafa alaka, neman shawara, da kuma jagoranci a harkokin mulkin gargajiya.
Bisa wannan, mai martaba Sarkin Ningi, tare da tawagarsa, ya kai ziyara ga Shehun Borno a fadarsa ranar Asabar a Maiduguri, Jihar Borno.
Da yake jawabi yayin ziyarar, mai martaba Sarkin Ningi Alh Haruna Yunusa Danyaya III, ya nuna godiyarsa ga Shehun Borno bisa goyon bayan da ya bai wa masarautar Ningi lokacin rasuwar marigayi Sarkin Ningi.
KARANTA WANNAN:
Bauchi: Masarautar Ningi Ta Yi Sabon Sarki
Gwamnan Bauchi Ya Sha Alwashin Cika Wasiyyar
Gwamnan Bauchi Ya Sallami Kwamishinoni Biyar
Ka Dakata Da Sake Fasalin Haraji- Gwamnan Bauchi Ga Tinubu
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Sarkin kan kafafen watsa labarai, Sadam Mato Burra, ya sanya wa hannu kuma ya raba wa manema labarai.
Sarkin ya bayyana cewa, ya shirya wannan ziyara ne don neman shawarar uba tare da yin alkawarin karfafa kyakkyawar alakar dake tsakanin masarautun biyu.
A nasa martanin, Shehun Borno ya yabawa Sarkin Ningi bisa wannan ziyara tare da karfafa shi da ya yi koyi da halayen marigayi Sarkin Ningi Alh Yunusa Muhammadu Danyaya, musamman nagarta, sadaukarwa, da kishin ci gaban masarautu da al’adun gargajiya.
Sarkin Ningi ya kuma kai ziyara ga Sarkin Fika, Dr. Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris CFR, wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan gargajiya na Jihar Yobe.
Haka zalika, Alhaji Haruna Yunusa ya ziyarci Sarkin Damaturu, Alhaji Dr. Shehu Hashimi II Ibn Umar Al-Kanemi, da kuma Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya OON, a fadojinsu ranar Lahadi a Jihar Yobe.
A yayin wannan ziyarar, sarakunan sun jaddada muhimmancin masarautun gargajiya wajen kawo cigaban al’umma tare da bayyana alkawarinsu na ci gaba da kiyaye al’adun gargajiya da karfafa hadin kai tsakanin masarautu.
Alh Haruna Yunusa, tun bayan nadin sa a matsayin Sarkin Ningi ya kai ziyara zuwa wasu masarautu da suka hada da Bauchi, Katagum, Misau, Jama’are, Dass, da Zazzau, a kokarinsa na karfafa dangantaka da neman hikimar gudanar da mulki.



