Hukumar tsaro ta Nigeria mai kula da gamagarin laifuka (NSCDC) reshen jihar Nasarawa, ta kama wani tsoho dan shekara 85 mai suna Ibrahim Haruna bisa zargin sa da laifin aikata lalata da wata yarinya ‘yar shekara 4.
An kama mutumin ne a unguwar Kongo da ke karamar hukumar Keffi a makon farko na watan Janairu.
Asirin Tsohon ya fara tonuwa ne a lokacin da wata ‘yar uwar wanda abin ya shafa ta lura da cewa yariyar na tafiya da kyar sannan kuma jini ya na fita daga tsakanin kafafun ta.
A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC, Jerry Victor, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yaudari yarinyar zuwa dakinsa yayin da babu kowa a gidan da ya ke zaune.
KARANTA: NSCDC Ta Kama Matashin Da Ya Yiwa Yarinya Yar Shekara 12 Fyade A Bauchi
An Tsare Ɗan Sanda Da Laifin Yiwa Budurwa fyade
Ana Zargin Wani Basarake Da Yiwa Yarinya Fyade A Jigawa
Kano : Kotu Ta Garƙame Mai Shagon Kemis Da Ya Yiwa Yarinya Fyaɗe
Wani rahoton likita ya tabbatar da cewa yariya an ci zarafin Yarinyar tare da bayyana lamarin a matsayin wanda ya ƙazanta.
Sai dai, duk da hujjojin da aka bayar, Ibrahim Haruna ya musanta zargin da ake yi masa, yana mai cewa an yi ma sa sharri ne.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya kasance makwabci ga gidan su yarinyar da ake zargin sa da cin zarafin ta.
Ana cigaba da tsare Tsohon a yayin da yarinyar ta ke samun kulawa a asibiti su kuma jami’an tsaro su ka cigaba da gudanar da binciuke.



