spot_imgspot_img

Jigawa: Yadda Kasuwancin Bandar Kwadi Ya Zama Hanyar Samun Kudin Shiga Ga Matasa

Kasuwancin bandar kwadi ya sauya rayuwar mutane da yawa a jihar Jigawa ta hanyar samar mu su da kudin shiga. Sai dai, duk da ribar da ma su wannan kasuwanci su ke samu, kasuwancin bandar kwadin ya kasance barazana ga muhalli.

Muhammad Isah, wani matashi mai shekara 32 da ya kammala karatun digiri, ya tsinci kan sa cikin kalubalen rashin samun aikin gwamnati bayan ya kammala bautar kasa.

Rashin samun aikin gwamnati ya tilasta Muhammad nemawa kan sa mafita, in da a karshe ya fara kasuwancin bandar kwadi, kasuwancin da ya sauya tarihin rayuwar sa.

“Ban samu aiki ba bayan na kammala karatu, haka na ke zaune babu abin yi. Daga baya na yanke shawarar shiga kasuwancin farautar kwadi domin na dogara da kai na. Da wannan sana’a yanzu na ke kula da iyali na,” kamar yadda Muhammad ya shaidawa wakilin WikkiTimes.

Muhammad ya ya ce yanzu haka ya na samun ribar N150,000 kowanne wata daga cinikin bandar kwadi tare da bayyana cewa yanzu shirin aure dan gina gida ya ke yi.

Muhammad Isah

Hadejia, daya daga cikin kananan hukumomin jihar Jigawa, ta kasance cibiyar kasuwancin kwadi. Kasuwancin bandar kwadi ya na kara samun karbuwa saboda karuwar bukatar naman kwadi a gida Nigeria da kasashen.

Yusufu Dapchi, wani mutum da ya shafe kusan shekara 20 ya na kasuwancin bandar kwadi, ya bayyana yadda harkar ta rufa ma sa asiri tare da matan sa biyu da ‘ya’ya ma su yawa.

“Na samu damar zuwa Hajji daga irin kudin da na samu daga wannan kasuwanci,” a cewar sa.

Sai dai, Yusuf ya bayyana cewa su na fuskantar kalubalen tsadar kayayyaki. “A baya mu na siyar da babban kwado a kan farashin N1,000 zuwa N1,500 amma yanzu farashin ya na kai wa har N6,500,” a cewar sa.

Yusuf Dapchi

Chibuke Alex, wani dan kasuwa a karamar hukumar Guri, ya bayyana yadda ya bar kiwon kifi tare da komawa kasuwancin kwadi tun shekara 15 da su ka wuce. Ya bayyana cewa kasuwancin kwadi ya fi na kifi riba.

Dan kasuwar ya bayyana cewa ya na samun ribar a kalla N15,000 a kullum, kudin da ya ce sun bashi damar kula da iyalin sa ba tare da fargabar rikicin manoma da makiyaya ko sauyin yanayi da ake fuskanta a jihar Jigawa ba.

SAMAR DA KUDIN SHIGA DA GINA TATTALIN ARZIKI

Ba iya daidaikun jama’a ne kadai su ke samun kudin shiga da gina tattalin arzikin su daga kasuwancin kwadi ba, hatta gwamnatin karamar hukuma ta na samun kudin shiga daga kasuwancin.

“Bayan ribar da ‘yan kasuwa ke samu, mu na samar da a kalla N90,000 kudin shiga ga karamar hukuma daga kudin lodi. Duk motar da ta yi dakon bandar zuwa kudu ta na biyan N30,000 kuma a wasu lokutan a kan yi lodin motoci fiye da hudu kowacce ranar Lahadi,” a cewar Godwin Idu, shugaban kungiyar ma su siyan bandar kwadi a Jigawa.

A cewar Godwin, kudin shigar da su ke samarwa karamar hukuma daga biyan kudin dako sun kai miliyan N1.4 a shekara.

Godwin Idu

Kazalika, ya kara da cewa direbobi da ke daukar ‘yan kasuwa da kayan su zuwa kudu su na samun ribar N60,000 zuwa N100,000 duk sati.

Ya kara da cewa bukatar naman kwadi na karuwa a kudancin Nigeria da kasuwannin kasashen ketare kamar su China, Amurka, da Turai.

KABULALE DA KULA DA MUHALLI

Duk da irin ribar da ke cikin kasuwancin bandar kwadi, akwai kalubale a tattare da harkar.

Bayan kalubalen rashin samun kwadi idan lokacin damuna ya wuce, ma su kasuwancin sun koka da rashin kayan aiki da yanayi mai kyau na kasuwanci.

“Kafin a cire tallafin man fetur, mu na biyan N14,000 a matsayin kudin mota na zuwa ko dawowa, amma yanzu kusan N30,000 mu ke kashewa,” a cewar Christina Akpepo, wata mai zuwa siyan bandar kwadi daga jihar Benue.

Kwararru a bangaren kula da muhalli sun yi gargadin cewa cigaba da farautar kwadi kan iya haifar da matsaloli ga muhalli da kuma samun rashin daidaito a halittun da ake da su a doron kasa.

“Akwai bukatar a dauki matakai domin kiyaye wuce kima wajen farautar jinsin kwadi domin neman kudi,” a cewar Audu Oseni, wani kwararre a bangaren harkokin muhalli.

Kwararru a bangaren abinci da cimaka sun bayyana cewa jiki ya na samun wasu muhimman sinadari daga naman kwadi, amma sun yi gargadin cewa akwai jinsin kwadi ma su guba.

A yayin da noman kwadi da kasuwancin namansu ya ke kara samun karbuwa, ana cigaba da yin kiraye-kiraye ga gwamnati a kan ta shigo harkar domin tabbatar da tsari da kuma dorewar ta.

‘Yan kasuwa da shugabannin al’umma su na neman gwamnati ta samar da kasuwa ko wani wuri na musamman domin kasuwancin bandar kwadi tare da bayar da tallafi ga ‘yan kasuwar da ke harkar.

“Akwai mutane fiye da 5,000, wadanda suka hada da ‘yan gari da baki da su ka dogara da kasuwancin kwadi,” a cewar Godwin.

Naziru Taura
Naziru Taurahttp://wikkitimes.com/hausa
Naziru Taura is a dedicated teacher, Hausa blogger, freelancer, and translator with a passion for education, information dissemination, and purposeful leadership. He specializes in crafting compelling stories in both English and Hausa, focusing on the Sustainable Development Goals (SDGs) and amplifying the voices of marginalized and underreported communities. Through his work, Naziru offers hope, advocates for justice, and drives meaningful conversations on societal progress. With over a decade of experience, Naziru has produced numerous impactful stories, shedding light on business and economic empowerment opportunities. His investigative work has also uncovered cases of corruption, abuse of power, and the mismanagement of public funds, showcasing his commitment to accountability and transparency.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories