Bauchi, da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, an dade ana girmama ta a matsayin cibiyar ilimin addinin Musulunci.
Malaman addinin da suka fito daga jihar sun taka muhimmiyar rawa wajen ilimantar da jama’a, da kuma kawo sabbin hanyoyi a koyarwar addini.
Wadannan malamai wadanda suka kware a wajen ilimantar wa ta hanyar gargajiya tare da sauya wa zuwa zamani ba wai kawai suna koyarwar Musulunci ba ne, har ma suna fuskantar matsalolin zamantakewa na yau da kullum, wanda hakan ya sa suka sami karbuwa a wajen miliyoyin mutane a gida da waje.
WikkiTimes ta zakulo fitattun mutane goma da ke taka rawar gani wajen koyar da addinin Musulunci, cigaban al’umma, da kuma tattaunawar addini a jihar Bauchi.
KARANTA WANNAN:
Manyan Malaman Najeriya 8 Da Suka Soki Taron Al-Qur’ani
Majalisar Malaman Bauchi Ta Yi Watsi Da Yunkurin Kafa Daular ‘SAYAWA’ A Tafawa-Balewa
SULEJA: Gwamnati Ta Dakatar Da Malamin Addini Daga Yin Wa’azin Da Karantarwa A Islamiyya
Ranar Da Ka Kashe Ni Kaima Ranar Zaka Mutu- Martanin Sheikh Idris Abdulaziz Ga Gwamnan Bauchi
Sheikh Ahmad Gumi Zai Gurfana Gaban Hukumomin Tsaro – Gwamnatin Tarayya
Sai dai, wannan jerin sunayen ba ya nufin sune kadai fitattun malamai ba, domin akwai da yawa da suke taka rawa.
Wadannan an zabe su ne bisa tasirin da suke da shi, shahara, da kuma yadda ra’ayoyinsu ke haifar da muhawara a kafafen yada labarai na gargajiya da na zamani.
Har ila yau, malaman da aka lissafo suna bin mazahabobi daban-daban kuma ba a lissafa su bisa kowace irin daraja ba.
1. Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Shi ne mafi girma kuma daya daga cikin shahararrun jagororin darikar Tijjaniyya a Afirka ta Yamma.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi fitacce ne a fagen tafsirin Al-Qur’ani, wanda ya fara tun 1948. An fara sanya karatukan sa a gidan radio mallakar jihar Bauchi a shekara ta (1976) da Radio Nigeria Kaduna a shekara (1980).
Ya yi aikin Hajji sau 55 da Umrah sau 205.
Baya ga ilimin addini, ya gina gidaje sama da 1,000 ga iyalansa da almajiransa, ya kafa makarantun Musulunci, kuma ya musuluntar da mutane da dama ta hanyar wa’azinsa mai hikima.
Ana girmama shi a matsayin jigon tafsirin Al-Qur’ani.
2. Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum
Ana kallonsa a matsayin gwarzon masu tsarkake zuciyar dan Adam da fadakarwa game da Allah.
Ya yi karatu a Najeriya, Libiya, Saudiyya, da Sudan, inda ya kware a Al-Qur’ani, Hadisi, da koyarwar Annabi Muhammad (SAW).
A matsayinsa na Babban Liman, yana yada koyarwar Al-Kitab wa Sunnah a cikin wa’azinsa da aikin da’awa.
Ya shahara da kuma dubban mabiya a cikin jiha Najeriya da ma wasu kasashen duniya.
3. Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi
Tawhidi (imanin tauhidi tsantsa) ya sa aka girmama shi, amma kuma hakan ya haifar da cece-kuce.
Ya yi karatu a Najeriya, Nijar, Saudiyya, da Sudan.
Kin bin wata kungiyar addini ya sa ya samu matsala da wasu kungiyoyin addini da kuma gwamnatin Bauchi, wanda ya kai ga daure shi da kuma fitar da shi daga jihar.
Duk da haka, yana da masu bibiyarsa sama da 100,000 a kafafen sada zumunta, kuma ya kafa kungiyar yan Banga mai suna Garu Security.
Ana kallonsa a matsayin mai da’awar tauhidi tsantsa.
4. Dr. Ibrahim Adam Disina
Sheikh Ibrahim Adam Disina malami ne, manomi, kuma fitaccen mai kirkirar kafafen yada labarai.
Ya yi karatu har zuwa matakin digirin digirgir duk da fitowa daga gida mai talauci.
Ya kammala karatunsa a Jami’ar Musulunci ta Madina, sannan ya kafa Sunnah TV.
Yana hada ilimi da noman dabbobi da aikin da’awa.
Wa’azinsa yana jawo hankalin jama’a daga kauyuka da birane saboda yana amfani da rayuwarsa a matsayin darasi.
5. Sheikh Salihu Sulaiman Ningi
Shi ne jagoran kungiyar Izala a Bauchi.
A matsayinsa na Shugaban JIBWIS (bangaren Jos), yana taka muhimmiyar rawa a tafiyar Izala.
Tafsirin Ramadan dinsa da kuma hudubobinsa a tarurrukan Izala na kasa suna jan hankalin dubban mutane.
Ya shahara a cikin ayyukan da’awa a kungiyar Izala a Arewacin Najeriya da ma kasashen makwabta.
6. Professor Mansur Isa Yelwa
Malamin Shari’a ne a Jami’ar Bayero da ke Kano.
Ya kware a bangaren ilimin Doka ta (Comparative Law) da Al-Qur’ani, kuma yana aiki da Salam Takaful Insurance.
Yana amfani da iliminsa wajen rubuce-rubuce da wa’azi domin fadakar da al’umma kan shari’ar Musulunci da kuma kasuwancin halal.
Yana da mabiya masu tarin yawa a kafofin sada zumunci a ciki da wajen Najeriya.
7. Professor Zubairu A. Madaki
Tafsirin Ramadan dinsa a Masallacin Umar bin Khattab yana jan hankalin mutane daga sassa daban-daban na kasa.
Ya yi digirinsa na Ph.D a Malaysia, inda ya kware a Al-Qur’ani da Hadisi.
Shi ne Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa’iqamatus Sunnah (JIBWIS) bangaren Kaduna a Bauchi.
A matsayinsa na malami a Jami’ar Jihar Bauchi, yana hada ilimi da wa’azi don cusa addini a rayuwar al’umma.
8. Sheikh Abul Fatahi Bauchi
Yana daga cikin manyan matasan da ke kare darikar Tijjaniyya ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.
Yana kare ayyukan sufi kamar Maulidi ta hanyar muhawara da malaman Izala.
Ana ganinsa a matsayin mai tsayin daka wajen kare darikar Tijjaniyya ta hanyar kafafen zamani.
9. Sheikh Junaid Abubakar
Shi ma dan darikar Tijjaniyya ne kamar Sheikh Abul Fatahi, amma yana da sassaucin tsanani fiye da shi.
Yana yin wa’azi cikin salo mai tausasa zuciya, yana yabon Annabi Muhammad (SAW), iyalansa da sahabbansa.
Bambancinsa da Abul Fatahi shi ne yana gujewa tsananin muhawara ko fada da sauran Maluman addini.
10. Malam Yahaya Jibril (Malam Mai Tauhidi)
Yana amfani da barkwanci wajen koyar da addini, wanda hakan ke sa ya shahara a tsakanin mata da matasa.
Yana jagorantar karatun Al-Qur’ani domin neman waraka da kuma fadakar da jama’a a yankunan karkara.
Ana kallonsa a matsayin malamin talakawa saboda yadda yake tafiyar da wa’azi cikin sauki da barkwanci.



