spot_imgspot_img

Rashin Hadin Kai Ya Dakile Cigaban Arewa – Sarkin Zazzau

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, Ya Bayyana Rashin Hadin Kai a Matsayin Babbar Matsala da Ke Fuskantar Ƙasa

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya bayyana cewa rashin hadin kai na daya daga cikin manyan dalilan da ke haddasa matsalolin da ƙasa ke fuskanta a yau.

Da yake jawabi yayin taron buda baki tare da Hakiman Zazzau, Sarkin ya nuna damuwa kan yadda rarrabuwar kawuna ke kara kamari a cikin al’umma, yana gargadin cewa hakan na iya haifar da matsaloli ga zuriya masu zuwa.

KARANTA WANNAN:

Sarakuna Sun Aika Sako Ga Masu Shirya Zanga-Zanga Bayan Ganawa Da Tinubu

Jerin Sarakunan Da Aka Hamɓarar Da Su Akan Ƙaragar Mulki Daga 1963 Zuwa Yanzu

Sarkin Ningi Ya Kafa Doka Ga Sarakunan Da Ke Tallafawa Masu Satar Mutane

“Duk abin da muke so shi ne mu hada kanmu, mu hadu mu yafewa juna. Idan mun batawa wani rai, to muna bada hakuri,” in ji shi.

Ya jaddada cewa hadin kai shi ne kadai hanyar da za ta tabbatar da ci gaban al’umma, yana mai gargadi cewa rashin hadin kai zai bar wa matasa da ‘ya’ya masu tasowa mummunan tarihi.

“Ta hanyar hadin kai ne kadai za mu iya ceto mutanen wannan gari. Idan har muka ci gaba da rarrabuwa, to muna barin wani yanayi mai muni ga aluma mai zuwa bayanmu,” ya yi gargadi.

Sarkin ya kuma nuna takaicinsa kan yadda abokai da ‘yan uwa da suka taso tare suka rabu, yana cewa, “Abin takaici ne yadda mutane da aka taso tare da su suka rabu, ba ka ganinsu, kuma ba ka damu da jin halin da suke ciki ba.”

Har ila yau, ya jaddada cewa wannan matsala ba ta tsaya a Zazzau kadai ba, illa iyaka ta shafi dukkan yankin Arewa gaba daya.

“Babu kyau a duk Arewa baki daya. Wannan ba abu bane da ya tsaya a Zariya, ko Jihar Kaduna, ko yankin Arewa maso Yamma kadai – dukkan yankin Arewa yana fama da wannan matsala,” in ji shi.

Taron buda bakin ya samu halartar dukkan Hakiman Masarautar Zazzau, tare da Sakataren Gwamnatin Jihar da ya wakilci Gwamna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories