spot_imgspot_img

Kananan Hukumomi 5 Da Suka Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya a Katsina

Kananan hukumomi biyar a jihar Katsina – Kurfi, da Jibia, da Batsari, da Safana da Danmusa – sun shiga yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga domin dakatar da rikice-rikicen da suka addabi al’ummominsu.

Yarjejeniyar ta fara ne a karshen watan Fabrairu a Jibia karkashin jagorancin Jibia People’s Forum, sannan aka ci gaba da irin wannan a Batsari da Safana, kafin daga bisani a watan Yuni mazauna Danmusa su kulla tasu yarjejeniyar a garin Bicci.

Shugabannin gargajiya, da dattawa, da jami’an tsaro da wakilan al’umma ne suka jagoranci tattaunawar, inda aka cimma matsaya kan kawo ƙarshen hare-hare da satar mutane. An kuma jaddada bukatar dawo da ’yan gudun hijira, da tabbatar da hanyoyin noma da sufuri sun sake buɗewa. Duk da haka gwamnatin jihar ta jaddada cewa ba ta shiga yarjejeniyar kai tsaye ba, sai dai ta bayyana cewa masu mika wuya za a basu damar komawa cikin al’umma.

Masu lura da al’amura da kungiyoyin farar hula sun bayyana cewa wannan mataki na iya zama sabon babi na kwanciyar hankali a Katsina, amma sun yi gargadin cewa dole ne a tallafa da gina makarantu, da samar da ayyukan yi da taimakon wadanda suka tsira daga rikicin, don gujewa dawowar tashin hankali a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories