Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis ta yanke wa Nnamdi Kanu, shugaban ƙungiyar IPOB da aka haramta, hukuncin daurin rai-da-rai bayan an same shi da laifukan ta’addanci.
Mai shari’a James Omotosho, wanda tun farko ya same shi da laifi a dukkan tuhume-tuhume guda bakwai da ake masa, ya ce Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da shari’arta ba tare da wata shakka ba game da laifukan ta’addanci da ake tuhumarsa da su.
A sakamakon haka, Justice Omotosho ya yanke wa Kanu hukuncin rai-da-rai a tuhume-tuhume na ɗaya, na huɗu, na biyar da shida, maimakon hukuncin kisa.
A cewarsa, rayuwa abu ne mai tsarki a wurin Allah.
Alkalin ya kuma yanke masa shekaru 20 a kan tuhuma ta uku, sannan ya yanke masa shekaru uku a tuhuma ta bakwai. (NAN)



