Dalibai 50 Na Makarantar ST. Mary’s Catholic Papiri Sun Kuɓuta Daga Hannun Masu Garkuw
Jimillar dalibai hamsin daga Makarantar ST. Mary’s Private Catholic Primary and Secondary School da ke Papiri a Jihar Neja, waɗanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su, sun kuɓuta kuma sun koma gida sun haɗu da iyayensu.
Wannan na faruwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu da ake zargi ’yan ta’adda ne suka kai hari suka kuma yi garkuwa da dalibai 303, inda wasu daga cikin su suka kuɓuta tsakanin Juma’a da Asabar suka kuma koma gida bayan kasa komawa makaranta.
Wannan bayani na cikin wani rahoto da Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Neja, Most Reverend Bulus Yohana, ya sanyawa hannu ta hannun mai taimaka masa a harkokin labarai, Daniel Atori, a Minna.
Sanarwar ta bayyana cewa sun tabbatar da wannan ne bayan tuntuɓar wasu iyaye da kuma kai musu ziyarar duba halin da suke ciki a gida.
Saboda haka, domin a rubuta adadi a fili, yanzu suna da dalibai 251 na firamare, dalibai 14 na sakandare, da malamai 12 da ke hannun masu garkuwa.
A halin yanzu, banda dalibai 50 da suka kuɓuta suka dawo gida, akwai dalibai 141 da ba a tafi da su ba lokacin harin.
Don haka, a jimlace, yanzu akwai dalibai 236, sannan wasu yara 3 ’ya’yan ma’aikatan makarantar, da dalibai 14 na sakandare, wanda gaba ɗaya ya zama yara 253 da kuma malamai 12 da ke hannun masu garkuwa.
A gefe guda kuma, Gwamnan Jihar Neja, Muhammed Umar Bago, yayin jawabi ga jama’ar jihar, ya ce ba su da cikakken bayani kan adadin dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su, amma hukumomin tsaro na aikin tantance adadin da ake aiki da shi kuma za a fitar da shi a hukumance.



