spot_imgspot_img

Sojoji Sun Cafke Dan Garkuwa da Mutane Yayin Neman Fansar Naira Miliyan 20 a Wukari, Jihar Taraba

Dakarun Brigade ta 6 ta Rundunar Sojin Najeriya, da ke aiki a ƙarƙashin Sector 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS) da Operation Zafin Wuta a Jihar Taraba, sun kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a ƙaramar hukumar Wukari.

Bisa sahihin bayanan sirri, dakarun sun cafke wanda ake zargin mai suna Umar Musa Geyi, a ranar 22 ga Nuwamba 2025 a yankin Jandei–Kulamu na Wukari, a lokacin da ake zargin yana tattaunawa da ‘yan uwa game da fansar Naira miliyan 20 domin sakin wanda aka yi garkuwa da shi.

A cewar mai magana da yawun Rundunar Sojin, Laftanar Umar Mohammed, wanda ake zargin ya daɗe a jerin waɗanda hukumomin tsaro ke nema, kuma ana zargin yana da alaƙa da wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke aiki a yankin Wukari.

Mohammed ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin na da hannu a sace Alhaji Jano, ɗan asalin Fulani na yankin Jandei–Kulala, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 13 ga Nuwamba 2025.

Ya ce har yanzu wanda aka sace yana hannun masu garkuwa.

Ya bayyana cewa dakarun sun kama mutumin ne bayan sun tare shi yana tattaunawa ta wayar salula, inda aka ji yana tabbatar da cewa wanda aka sace yana hanun su, tare da neman fansar Naira miliyan 20 kafin a sake shi.

Mai magana da yawun rundunar ya ƙara da cewa wanda ake zargin yana tsare yana fuskantar ƙarin bincike domin gano inda wanda aka sace yake da kuma taimakawa wajen ci gaba da aikin ceto.

A halin da ake ciki kuma, Kwamandan Brigade ta 6, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa dakarun bisa yadda suka nuna ƙwarewa, tare da sake nanata aniyar rundunar na tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifi a fadin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories