Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci a janye jami’an ‘yan sanda da ke bai wa manyan mutane (VIPs) kariya a fadin kasar.
Wannan sanarwar ta fito ne daga Bayo Onanuga, Mai Ba wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Bayanai da Tsare-tsare, a wata takarda da ya fitar ranar Lahadi.
Onanuga ya ce daga yanzu, hukumomin ‘yan sanda za su mayar da jami’an zuwa ainihin aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya ce an bayar da wannan umarni ne a wurin taron tsaro da Shugaba Tinubu ya gudanar da shi a ranar Lahadi tare da shugabannin rundunar ‘yan sanda, sojojin sama, sojojin kasa da Darakta Janar na Hukumar DSS a Abuja.
A cewar umarnin shugaban kasa, wadanda ke bukatar tsaron ‘yan sanda daga cikin VIPs za su nemi jami’an tsaro masu dauke da makamai daga Hukumar Tsaro ta Farar Hula (NSCDC).
A yankuna da dama a Najeriya, musamman karkara, babu isassun jami’an ‘yan sanda a cibiyoyin su, lamarin da ya rage karfin kare jama’a yadda ya kamata.
Saboda kalubalen tsaro da ake fuskanta a yanzu, Shugaba Tinubu ya umarci a karfafa kasancewar ‘yan sanda a dukkan al’ummomi.
Onanuga ya kara da cewa Shugaba Tinubu ya amince da daukar karin jami’an ‘yan sanda 30,000.
Gwamnatin tarayya kuma tana aiki tare da jihohi domin inganta cibiyoyin horas da ‘yan sanda a fadin kasar.
Taron ranar Lahadi ya samu halartar Shugaban Rundunar Sojojin Kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu; Shugaban Rundunar Sojojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun; da Darakta Janar na DSS, Tosin Adeola Ajayi.



