spot_imgspot_img

’Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an ’Yan Sanda Biyar,  Sun Jikkata Wasu A Bauchi

An kashe jami’an ’yan sanda biyar, yayin da wasu biyu suka ji rauni sakamakon wani kwanton bauna da aka yi wa tawagar hadin gwiwar rundunonin ’yan sanda yayin sintiri a kauyen Sabon Sara da ke karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi.

Jami’an sun shiga aikin dakile rikicin manoma da makiyaya ne lokacin da suka gamu da harin da ake zargin ’yan bindiga suka kai, wanda ya janyo musayar wuta da ta yi sanadiyyar hallaka wasu daga cikin maharan.

A cewar Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, tawagar sintirin da ta kunshi RRS, 10PMF, Sashen Yaki da Garkuwa da Mutane da kuma Sashen Bincike na Jihar, ta gamu da kwanton baunan wasu matasa dauke da makamai da ba a tantance ba.

Ya tabbatar da cewa wadanda suka rasa rayukansu sun hada da DSP Ahmad Muhammad, ASP Mustapha Muhammad, Inspector Amarhel Yunusa, Inspector Idris Ahmed da Corporal Isah Muazu, yayin da wasu biyu ke samun kulawar likitoci.

Kwamishinan ’yan sanda, CP Sani-Omolori Aliyu, wanda ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, ya jajanta wa iyalan jami’an da suka mutu, tare da tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin gano wadanda suka aikata laifin da gurfanar da su, yana sake nanata kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories