A wani muhimmin lamari da ya ja hankalin jama’a, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a mazaɓarsa da ke Jada, Jihar Adamawa.
Rahotanni sun nuna cewa Atiku ya karɓi katin ne bayan kammala shiri da tattaunawa da manyan jagororin jam’iyyar, lamarin da ke nuna sabuwar hanyar siyasar da yake shirin ɗauka a gaba.
Wannan mataki ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasa, inda ake kallonshi a matsayin sabon babi a harkokin jam’iyyun Najeriya da kuma shirya shiryen siyasar da ke gabatowa.


