spot_imgspot_img

Sheikh Dahiru Usman Bauchi Ya Rasu Bayan Doguwar Jinya

Fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu a daren Alhamis bayan dogon jinya na tsawon lokaci sakamakon tsufa

Ɗaya daga cikin ƴan uwa na kusa, M. Daha Azhary Bauchi, ya tabbatar da rasuwar, yana cewa: “Innaa lillahi wa innaa ilaihi raaji’un… Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi wafati yau Alhamis 27-11-2025. Allah ya bamu albarkansa.” Wani almajirinsa, Malam Garba, shima ya tabbatar da labarin.

Sheikh Dahiru Bauchi, wanda ya rayu tsawon kusan shekaru dari, ya shahara wajen karantar da Al-Qur’ani, da gina ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya da ƙasashen maƙwabta. Miliyoyin mabiyansa suna ɗaukarsa a matsayin ginshiƙi wajen yaɗa ilimin ɗariƙa.

Ana ci gaba da shirya jana’izarsa a wannan lokaci, kuma za a sanar da cikakkun bayanai nan gaba.

Za mu’ kawo karin bayani nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories