A jiya Alhamis ne Sheikh Dahiru Usman Bauchi, jagoran ɗarikar Tijjaniya a Najeriya, ya rasu, lamarin da ya jefa mabiya Tijjaniya cikin alhini, sannan yau Juma’a aka yi jana’izarsa a garin Bauchi. Bayan mutuwarsa, Sheikh Bappa Hotoro ya gabatar da karatu inda ya bayyana abubuwan da ya kira bidi’o’i da aka aikata a lokacin gudanar da jana’izar marigayin malamin
Sheikh Bappa ya fara da bayyana cewa jinkirta binne Sheikh Dahiru zuwa washe gari bai yi daidai da koyarwar sunnah ba, domin ya kamata a hanzarta binne mamaci tun daga lokacin da aka tabbatar da mutuwarsa. Ya ce wannan jinkiri na ɗaya daga cikin abubuwan da ya yi Allah-wadai da su.
Ya kuma yi tsokaci kan abin da ya bayyana a matsayin bidi’a mafi muni, wato binne marigayi a cikin masallaci. Bappa Hotoro ya tunatar da cewa Manzon Allah ya hani yin kabari a cikin masallatai, yana mai cewa yin haka kwaikwayon al’ummomin da ba musulmi ba ne, wadanda ke amfani da wuraren ibada wajen binne matattu.
Sheikh Bappa Hotoro ya jaddada cewa wajibi ne musulmai su kiyaye bin dokokin sunnah musamman a lokutan jana’iza, domin kauce wa aikata abubuwan da ba su da tushe a addini. Ya buƙaci al’umma da su koyi natsuwa da bin koyarwar shari’a a duk wani abu da ya shafi mutuwa da jana’iza.



