Bayan Mako Biyu Da Aure Ango Ya Gano Amaryarsa ​​Namiji Ne

Wani malamin addinin Islama mai suna Mohammed Mutumba ya kaɗu bayan da ya gano cewa sabuwar matar da ya aura kuma ya kwashe mako biyu yana zaune da ita, ashe namiji ne.

Mutumba ya haɗu da Ms Swabullah Nabukeera a masallacin da ya je ya yi sallah, nan take ya fara soyayya da ita, in ji Daily Monitor, wata kafar yada labarai ta Uganda.

A ƙarshe ma’auratan sun yi musayar alƙawuran aure a ƙarƙashin addinin Musulunci.

Sai dai kuma sabbin ma’auratan da ba su yi jima’i ba kafin aurensu, su ma sun shafe mako biyu bayan yin auren nasu, ba tare da saduwar aure ba, domin “amarya” ta yi iƙirarin cewa tana haila. Mutumba yace ya hakura ya jira ta kammala hailar.

Asirin “amarya” ya tonu ne bayan da maƙwabcin Mutumba ya yi iƙirarin cewa sabuwar matar tasa ta tsallaka ta katanga ta sace musu talabijin da tufafi. Makwabcin ya kai rahoton lamarin ga ofishin ƴan sanda, inda daga nan ne aka tura jami’an tsaro su kamo uwargida Nabukeera.

Jami’in binciken manyan laifuka na gundumar Kayunga Mista Isaac Mugera ya ce a lokacin da amarya Nabukeera ta isa ofishin ƴan sanda tana sanye da hijabi da takalmi.

“Kamar yadda ƴan sanda suka saba, wata ƴar sanda mace ce ta binciki wanda ake zargin sosai kafin ta kai shi dakin da ake tuhuma. Sai dai kuma abin ya ba jami’ar mamaki, inda aka gano cewa wadda ake tunanin mace ce, a zahiri namiji ne wanda ya cusa tufafi a cikin rigar nono don yaudarar cewa nono na gaske ne,” in ji Mugera.

“Da aka ci-gaba da bincike, mun gano cewa wanda ake zargin yana da al’aurar maza. Nan da nan muka sanar da “maigidanta” wanda ya raka ta ofishin ƴan sanda,” in ji shi.

Labarin ya girgiza Mutumba wanda ya nemi ƴan sanda da su bar shi ya tabbatar da kansa ta hanyar ba shi damar ganin al’aurar “matarsa”.

Da ya gano cewa lallai namiji ne, Mutumba ya tayar da hankali inda ya zargi Nabukeera da laifin sata.

Mugera ya ce daga baya sun yi wa Ms Nabukeera tambayoyi, wanda ya bayyana Richard Tumushabe ne sunansa na ainihi, kuma yana da shekaru 27.

Mugera ya ƙara da cewa Tumushabe ya shaidawa ƴan sanda cewa ya yaudari Mutumba cewa shi mace ce a kokarinsa na neman kuɗinsa kawai.

“Mun riga mun zarge shi da laifin satar shaida, sata da kuma samun kaya ta hanyar yaudara,” in ji shugaban CID. Da yake ba da labarin yadda ya yi soyayya da wanda ake zargin, Mutumba, limamin masallacin Kyampisi, ya ce ya samu Tumushabe a masallacin Kyampisi inda ya je yin sallah.

“Ina neman matar da zan aura, sai na sauka a kan wata kyakkyawar yarinya sanye da hijabi, sai na buƙaci mu yi soyayya, kuma ta amince. Mun yi soyayya, duk da haka, ta gaya min cewa ba za mu iya yin jima’i ba har sai na ba iyayenta sadaki kuma na yi musayar alƙawarin aure,” in ji Mutumba.

Ya bayyana cewa a cikin mako guda ya kammala komai sannan ya ziyarci kanwar Nabukeera, Misis Nuuru Nabukeera, mazauniyar ƙauyen Kituula a ƙaramar hukumar Seeta-Namuganga.

Kawar Tumushabe, wacce ita ma ƴan sanda suka kama ta, ta ce Mutumba ya biya sadaki da suka haɗa da awaki biyu, buhunan suga biyu, katon ɗin gishiri da kuma Al Ƙur’ani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories