Ƴan Sandan Jihar Kano Sun Daƙile Wani Shirin Kai Hari A Ranar Sallah

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da gano tare da daƙile barazanar kai hari da wasu mutane suke shirin yi a sirrin ce a ranar sallah.

 Kwamishinan ƴan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel, a wata ganawa da ya yi da malaman addinin musulunci da kuma wakilai daga masarautun Kano guda biyar a ranar Litinin din da ta gabata, ya ce ƴan sanda sun gano wasu mutane da ke gudanar da ayyukansu a cikin kungiyoyin musulmai domin tada tarzoma.

Kwamishina Gumel ya kara da cewa rundunar ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar sun gaggauta kawo daƙile shirin kai harin da aka yi shirin yi dama wanda ake ƙoƙarin yi lokacin bukukuwan  Sallah da kuma bayan sallah.

 Ya bayyana  mutanen da ke kokarin aikata ta’asar da ƙaryar cewa su ƴan Qadiriyya ne,duk da cewa shugaban darikar, Sheikh Qaribullah Kabara ya nesanta kansa da waɗannan mutane ta hanyar  nuna goyon bayan zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories