Sheikh Bappa Hotoro ya jaddada cewa wajibi ne musulmai su kiyaye bin dokokin sunnah musamman a lokutan jana’iza, domin kauce wa aikata abubuwan da ba su da tushe a addini. Ya buƙaci al’umma da su koyi natsuwa da bin koyarwar shari’a a duk wani abu da ya shafi mutuwa da jana’iza.
Wasu mutane na ɗaukan cewa bai dace mace mai juna biyu ta ci gaba da yin jima’i ba. Amma masana lafiya sun bayyana cewa yin jima’i da mace mai ciki yana da fa’idodi da dama ga lafiyarta da kuma cigaban cikin da take ɗauke da shi, muddin babu wata matsala ta likita da ta hana hakan.
Jami’ar ta bayyana lamarin a matsayin taron Damfara da aka shirya ba tare da saninta ba, duk da cewa manyan baƙi ciki har da Gwamnan Katsina, Dikko Radda, sun halarta.
Zaman na dogon lokaci kamar zama a ofis, ko kallo ko amfani da waya ba tare da motsa jiki ba yana rage yawan kuzarin da ake ƙonewa. Wannan yana sa kitse ya taru nan da nan cikin sauƙi.