TSOFAFFIN GINE-GINEN TARIHI: Rushewar Masallacin Juma’a Na Zariya

Daga Haruna G. Magashi Esq

Babu shakka tsofaffin garuruwan mu a nan Arewa su na dauke da gine-gine masu dimbin tarihi wadanda suka zama abin alfaharinmu. Za ka iya hangen Hasumiyar Gobarau a Birnin Katsina, ko ka je Bauchi ka ga tsohon masallacin da yake tun kafin zuwan Turawa, ga gidan Makama a Kano da Masallacin Juma’a wanda Sarki Bayero ya gina shi cikin 1940s ko wasu gine-gine dai musamman a cikin gidajen sarauta.

Mun kasance muna kiyaye wadannan gine-gine saboda tarihin da suke dauke da shi, muna alfahari da zamansu muna daukar matakan kiyaye su da tabbatar da ba a salwantar da su ba, madalla da wannan tarihi.

Idan muka waiwaya kuma za mu iya ganin wani abu dake tattare da wadannan tsofaffin gine-ginen tarihi. Tsufa su da dadewar su yana sa su yi rauni har su iya zama barazana ga lafiyar mu da ma rayuka.

Wannan shi ne abin da ya faru a Zaria ranar Juma’a, inda lokacin Sallar La’asar tsohon Masallacin Juma’a na Kofar Fadar Sarkin Zazzau ya rufto akan masallata, inda kimanin mutane 10 suka rasu.

Me Ya Jawo Wannan?

Masallaci ne mai tsohon tarihi, duk da an sabunta shi, amma ya dade a haka. Watakila da za a tambayi injiniyoyi, za su ce ya kai shekarun da ya kamata a sabunta shi. Haka gine-gine suke, suna da lokacin da ya kamata a sabunta su. Ko da gada da aka gine a yanzu, akan ce za ta yi shekara kaza, kamar gadar Gidan Murtala ta Kano, an yi ta za ta yi shekara 80, idan lokacin ya yi, to dole a sabunta ta.

Mu dauki misalin Masallacin Juma’a na Kano, Sarki Bayero ne ya gina shi cikin 1940s, yanzu maganar da ake, ya kai shekara 80. To! Akwai shiri da ake yi na sabunta shi? Ko sai dai kwaskwarima kawai da ake masa? Ko ana ganin ya zama gini na tarihi da ake kira ‘Monument’ wanda ba za a so a taba shi ba? Ba a hangen tsufansa da dadewar sa yana bukatar sabunta shi?

Shawara:

Ya dace irin wadannan gine-gine a samu injiniyoyi su rika duba su, su ga kwarin su, sannan su bada shawarar abin da ya kamata a yi musu, wannan zai taimaka wajen kare afkuwar ire-iren abin da ya faru a Zariya na ruftowar masallaci.

Da fatan za a duba, Allah Ya jiƙan wadanda suka rasu, Ya ba masu rauni lafiya. Allah Ya kare afkuwar irin wannan a gaba

Haruna G. Magashi Esq marubuci ne, lauya kuma ɗan siyasa. Za a iya samun sa ta shafin sa na harunmagashiesq.wordpress.com ko ta imel: [email protected]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories