Aliko Dangote Ya Faɗo Daga Matsayin Wanda Ya Fi Kowa Kuɗi A Afrika

Hamshaƙin dan kasuwar nan na Najeriya Aliko Dangote ya yi ƙasa a jerin masu kudin nahiyar Afrika inda ya fado daga mataki na 1 zuwa 2, in ji mujallar Forbes.

Mujallar Forbes ta ce a yanzu dai Aliko Dangote ya zama mutum na biyu mafi arziki a Afirka bayan da hamshakin attajirin nan na kasar Afirka ta Kudu Johann Rupert ya zama attajirin da ya fi kowa kuɗi a Nahiyar Afrika.

Mujallar Forbes ta bayyana cewa Aliko Dangote ya koma matsayi na biyu bayan da dukiyarsa ta ragu daga Dala Biliyan 13.5 a shekarar 2023 zuwa Dala biliyan 9.5 a farkon shekarar 2024.

Hamshakin attajirin ya shekara fiye 10 a matsayin attajirin Afrika tun shekarar 2013, kamar yadda alƙalumman jaridar Bloombarg kan attajiran duniya ya nuna.

Za a iya danganta faduwar darajar Naira da sauran batutuwan da suka shafi tattalin arziki da raguwar arzikin Dangote.

Ga Jerin Attajirin Nahiyar Afrika da Mujallar Forbes ta fitar kamar haka:

Johann Rupert & Family $10.3 billion
Aliko Dangote $9.5 billion
Nicky Oppenheimer & Family $8.3 billion
Nassef Sawiris $7.4 billion
Abdulsamad Rabiu $5.9 billion
Nathan Kirsh $5.8 billion
Issad Rebrab & Family $4.6 billion
Mohamed Mansour $3.6 billion
Naguib Sawiris $3.3 billion
Mike Adenuga $3.1 billion

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories