WTT Doha 2023: Aruna Quadri zai kara da Hugo Calderano na Brazil a wasan farko.

Dan wasan kwallon tebur Tennis mai lamba ta daya a Afirka, Aruna Quadri zai kara da mai lamba ta 5 a duniya Hugo Calderano na Brazil, a wasansa na farko na kakar wasa ta bana, a gasar kwallon tebur tennis na maza da za a yi a Doha da ke Qatar, daga 3 zuwa 5 ga watan Janairu.

Gasar dai za ta kunshi manyan ‘yan wasan kwallon tebur tenis  masu lamba ta 1 zuwa 16 a duniya wanda za su fafata domin samun nasarar lashe kofin.

Aruna shi ne dan wasan Afrika daya tilo da zai barje gumi a gasar tun farkon gasar a shekarar 2021, a wannan shekarar ta 2024 kuma, Aruna shi ne dan wasa mafi karanci mataki da zai shiga gasar.

Fitaccen dan wasan da Aruna ya yi shi ne a shekarar 2022 lokacin da ya doke Liang Jinkhun na kasar Sin mai lamba shida a duniya a wancan lokaci, inda ya kai matakin yan wasa takwas na karshe na gasar.

A karshe ya yi rashin nasara a wasan daf da na kusa da karshe a hannun Hugo Calderano na Brazil wanda shi ne abokin karawarsa a wannan zagayen na farko a bana. Ana sa ran zai yi iya bakin kokarin sa don samun damar zuwa matakin kwata final ko kuma ya yi wani kyakkyawan bajinta a bana.

A halin yanzu Aruna shine dan wasa mafi karanci mataki/lamba na 16 a duniya da maki 1175 shi kuma abokin karawarsa Hugo Calderano yana matsayi na 5 da maki 2875.

Ana sa ran gudanar da wasan a ranar Laraba da karfe 10:30 na safe

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories