Na Yafe Fansho Ɗina Ku Daina Biyana – Dankwabo Ya Faɗi Wa Gwamnatin Gombe

Tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata da ke wakiltar mazaɓar Gombe ta arewa, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya buƙaci gwamnatin jihar da ta dakatar da biyansa kuɗin fansho na wata-wata da yawansu ya kusa kai wa dubu ɗari bakwai.

Dankwambo a wata wasiƙa da ya aike wa gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya mai kwanan wata 4 ga Oktoba da Wakilinmu ya ci karo da kwafinta a ranar Litinin, ya ce, biyansa fansho na wata-wata ya samu amincewa ne ƙarƙashin dokar mulki ta fansho na shekarar 2007.

A cewarsa, a kowace wata, gwamnatin jihar na biyansa kuɗin fansho da ya kai naira N694,557 a matsayinsa na tsohon gwamna, ya ƙara da cewa, biyo bayan shawarori da ya yi da ƙungiyoyin fararen hula, cibiyoyi, abokai da ‘yan uwa, ya amince da daina karɓan kuɗin fanshon haka nan.

“Don haka na ke rubuta maka buƙatar ka dakatar da biyana fansho/alawus ɗin naira N694,557.82 da ake biyana a matsayin tsohon gwamnan jihar Gombe.”

Sanata Ibrahim, ya ƙara da cewa, tun lokacin da ya sanya ƙafarsa ya bar ofishin gwamnan jihar, ba ya samun cin gajiyar fakej-fakej na wasu tsarin cin gajiya da suka ƙunshi kiwon lafiya, kuɗaɗen zirga-zirga da kuma na kwaskwarima ga kayan ɗaki.

A cewarsa: “Kuma yana da kyau a lura, tun lokacin da na bar ofis a shekarar 2019, ban taɓa amfana da wani tagomashin kula da kiwon lafiya, kwaskwarimar kayan ɗaki, zirga-zirga da sauransu ba,” wasiƙar ta karanto a wani ɓangare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories