‘Yan Sanda Sun Hallaka Ɗan Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Mutun 6 A Bauchi

Jami’an tsaron ‘yan sanda a jihar Bauchi sun yi musayar wuta tsakaninsu da masu garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Toro inda suka hallaka ɗan garkuwa da mutane 1 da ceto mutum shida da aka yi garkuwa da su ciki har da wata budurwa ‘yar shekara 17 Rashida Hamisu daga maɓoyar ‘yan fashin dajin.

A ranar 1 ga watan Nuwamban 2023 ne jami’an ‘yansandan da haɗin guiwar JTF gami da mafarauta suka samu wani rahoton maɓoyar masu garkuwa da mutane da suke dazuka biyu da aka gano a Angwari da Sara.

A sanarwar manema labarai da kakakin hukumar, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar wa ‘yan jarida a ranar Alhamis, ya ce, tawagar sun yi musayar wuta wanda suka sha ƙarfin masu bindigan har ta kai sun kashe ɗaya sauran kuma sun arci na kare ɗauke da harbin bidigogi a jikinsu, kuma sun tarwatsa maɓoyar nasu.

Ya ce, an kwashi waɗanda aka ceto zuwa babban asibitin Toro domin nema musu kulawar likitoci gami da maida su ga iyalansu cikin ƙoshin lafiya.

Kazalika, ‘yan sandan sun kuma samu wani rahoton da ke cewa wasu ‘yan bindiga sun farmaƙi direban hukumar kula da inganci kayayyaki (SON) da ke Bauchi tare da sace mota ƙirar Toyota Hilux Bus mallakin hukumar.

A cewarsa, ‘yan sandan sun ci karo da motar a kan hanyar Maidugiri inda suka kamota. 

A cewarsa, lokacin da waɗanda suke cikin motar da ake zargin ɓarayi ne da yawansu ya kai uku suka hangi ‘yansanda, nan take suka bar motar suka arci na kare.

Wakil, ya naƙalto cewa, direban motar mai suna Sani Ahmed, ya shaida musu cewa yana dawowa daga wani aiki da ya je yi a Azare zuwa cikin garin Bauchi ne bayan da ya sauqe wani abokin aikinsa, Mohammed Mohammed a gidansa da ke GRA kwatsam sai wasu suka tare shi a lokacin da ke dawowa bayan da ya tsaya sayen kosai, inda suka nuna masa bindigogi ƙirar Fistol tare da neman ya ba su motar ko su kasheshi.

Bisa barazanar da suka yi masa ne ya basu damar kwace motar da arcewa da ita.

Motar dai ‘yansanda sun dawo da ita daga kan titin Maiduguri inda ake zargin ɓarayin sun yi ƙoƙarin barin jihar da ita.

Wakil ya ce, yanzu haka su na kan bin sawun ɓarayin domin tabbatar da kamosu yayin da bincike ke ci gaba da gudana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories