Sheikh Dahiru Bauchi Ya Buƙaci A Gaggauta Ƙaddamar Da Bincike Kan Kisan Masu Maulidi A Kaduna

Shaikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi tir da Allah wadai da kisan da sojoji suka yi wa masu maulidi da cewa hakan kan ya faru ne bisa ‘kuskure’, inda ya misalta hakan da babban sakacin da bai kamata ya faru ba.

Dahiru Bauchi a saƙon jajensa da ya aike wa musulman duniya kan kisan masu Maulidi ƙauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna da ake zargin mutum kusan 85 sun rasa rayukansu yayin da wasu sama da 50 suka jikkata a daren ranar Lahadi yayin da suke zaman tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad wato Maulidi.

Shehin ya buƙaci gwamnati da ta gabbata kafa kwamitin bincike da zai gano waɗanda suka aikata hakan domin hukunta su.

A cewarsa, koda sojojin sama sun ce ba su da masaniya kan kisan, amma alhakin kula da yaƙi ta sama na wuyarsu don haka su ma akwai sakacinsu, ya kuma ɗaura laifin ga sojojin sama da na kasa da kuma gwamnati.

Kazalika, babban malamin ɗarikar ya nemi gwamnati ta biya diyyar masu maulidin da suka rasa rayukansu sakamakon ruwan bama-bamai da sojoji suka yi musu.

A cewarsa: “Ina yin ta’aziyya ga dukkanin musuluman duniya da musulman Afrika da musulman Nijeriya a kan abun da ya faru, wanda ya faru a Kaduna mun bincika sun ce wai ba jiragen saman sojojin Nijeriya ba ne, sojojin kasan Nijeriya ko sun ce su ne, to ai su babu dama su hau sama. Saboda haka mun yi mamakin yadda aka rasa rayuka.”

Ya ce, babban mai laifi kan wannan lamarin ita ce gwamnati domin ita ce ta yi sake.

“Haƙiƙa mun ji zafi! mun ji zafi!! kuma muna yin ta’aziyya ga dukkanin musulmai na duniya bisa ga wannan rashin da muka yi.”

“Mun kuma yi mamakin yadda sojojin saman Nijeriya suka ce ba su san da harin ba, mun yi mamaki yadda suka hau soma suka sako bam kan mutane. Mun yi mamakin yadda aka ƙona kusan mutum ɗari. Wannan haƙiƙa ya yi yawa.”

Ya ce, wannan babban sake ne da ya kama tun daga kan sojojin sama domin a cewarsa su ne ke da alhakin kula da yaƙin sama, da su kansu sojojin kasan haɗi da ganin laifin gwamnati kan harin da ya farun.

Ya yi kira ga gwamnati da ta gaggata kafa kwamiti domin binciko ta yadda lamarin ya faru da har aka kashe mutane kusan 100.

“Muna neman su sanar da mu yadda aka ƙona mana masu maulidi a jirgin sama. Mun ji zafi matuƙa. Gwamnati tana nan tana kallo aka yi wannan abun a gabanta, don haka muna neman ta biya diyya na mutanenmu masu maulidi,” Sheikh Dahiru ya shaida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories