Ban Aike Da Wata Wasiƙa Kan Shari’ar Gwamnan Kano Ba – Dahiru Bauchi

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi hannun riga da wata wasiƙa da aka yaɗa a kafafen sadarwar zamani da ke cewa ya aike da wasiƙa ga alkalin alkalan Nijeriya da ke kiransa da ya shiga cikin shari’ar kujerar gwamnan Kano.

A wasiƙar da aka yaɗa aka kuma sanya sunan Shaikh Dahiru da cewa shi ne ya sanya hannu na bogi, an buƙaci Alkalin Alkalan da ya tabbatar da an yi gaskiya da adalci wajen yanke hukunci a kotun koli kan zaɓen kujerar gwamnan jihar Kano domin kauce wa yin hukuncin da ka iya janyo tashin hankali ko wani yaƙi.

Sai dai a wani saƙon sautin murya da Sheikh ya fitar, ya ƙaryata batun wasiƙar, inda ya ce sam ba daga wajensa hakan ya fito ba.

“Ba ni na rubuta wasiƙar ba, ban santa ba. Ban san takardar ba, ba ni ne na rubuta ba.

“Ban san takardar ba, ba daga ni take ba,” ya sake nanatawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories