Rahoto Na Musamman: Duk Da Irin Maƙudan Kuɗaɗen Da Ake Warewa Tsaro A Zamfara Amma Har Yanzu Matsalar Na Cigaba Da Ta’zzara

Har yanzu ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai suna ci gaba da cin karen su ba babban inda su ke kai hare-hare a yankunan jihar Zamfara duk da cewa akwai jami’an tsaro da dama waɗanda suka haɗa da sojoji ƴan sanda ,jami’an tsaron farin kaya, da na Civil Defence da kuma sabuwar rundunar kare al’ummar Zamfara da aka ƙirƙirar mai suna (Askawaran Zamfara).

 Tabarbarewar tsaro da jihar ke fama da ita ya sauya daga kai hari da buya zuwa yakin sari-ka-noke inda kai tsaye ƴan fashin ke kai farmaki kan al’umma tare da komawa maboyarsu ba tare da fuskantar ƙalubale ba.  Wannan ne ya sa jami’an tsaro suka zama yan sanda,Ƴan banga, da sarakunan gargajiya suka zama abu na farko da ake kaiwa hari.

Mazauna yankunan da ake yawan  kaiwa hari sun shaida wa WikkiTimes cewa ‘yan bindigar kan kai irin wadannan hare-hare ne da sanyin safiya ko kuma maraice.

 Sun yi nuni da cewa, waɗannan ƴan bindiga suna kai munanan hare-hare, inda suke kashe duk wanda ya kawo musu tsaiko, suna sace mata da ƙananan yara tare da kona dukiyoyi, musamman kayan abinci.

 “Jiya da yamma da misalin karfe 5 na yamma sun zo,kai tsaye suka wuce cikin garin, suka nufi wani ƙauye, mun sha za su kai hari wannan kauyen ne, amma abin ya ba mu mamaki inda muka ga sun nufi.  garin Zurmi.Yayin da suka fita daga cikin gari sai kawai suka fara harbi ba da jimawa ba suka nufi ofishin ƴan sanda da ke garin na Zurmi”.  Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa WikkiTimes.

“A nan suka kashe DCO tare da raunata wasu jami’an ƴan sanda.  Sun bincike ko ina suna neman ƴan uwansu da ‘yan banga suka kama amma ba su same su ba.  Daga nan suka ci gaba da gudanar da harbe-harbe ba tare da wani ƙalubale ba wanda hakan ya ɗauki sama da awa ɗaya.  Muna da rukunin sojoji amma sun kasa yin komai .Suna maida tsagaita ne kawai lokacin da sojoji suka fito a wajen garin”, wata majiya da ba a bayyana sunanta ba ta fada wa WikkiTimes ranar Litinin.

 Harin da aka kai ofishin ƴan sanda a Zurmi ya yi sanadiyar mutuwar mutane bakwai yayin da aka yi garkuwa da da yawa.

 Harin dai yayi kama da harin da suka taɓa kaiwa a ranar Talata 13 ga watan Disamba inda aka yi garkuwa da mutane 15 tare da kashe mutum ɗaya.

 WikiTimes ta fahimci cewa, harin na baya-bayan nan wanda ya faru a ranar litinin ya biyo bayan wani harin da aka kai da rana a garin a ranar Talatar da ta gabata inda mazauna garin suka shagali suna hada hada a cikin kasuwar inda wannan hari ya yi sanadiyyar raunata mutane da dama tare da yin awon gaba da wasu da dama kamar yadda majiyar ta tabbatar wa wakilinmu.  Inda aka bayyana cewa ƴan bindigar sun dawo ne bayan kwana ɗaya da suka kai wani mummunan hari.

Hare-Haren nan Ba Zurmi kadai ake kai su ba.

Duk da cewa gwamnatin tarayya ce ke ba da tallafin tsaro, yawanci su ma jihohi sun yi alkawarin tabbatar da tsaroon, galibi suna tallafawa hidimomin cikin ggia don kara yunƙurin gwamnatin tarayya.

 A shekarar 2023, jihar Zamfara ta ware Naira biliyan 3.8 ga ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida, amma sai dai Naira miliyan 590.3 kawai aka kashe.

 Jihar ta yi shirin kashe Naira biliyan 1.8 daga cikin kasafin tsaro da na cikin gida na shekarar 2023 a kan manyan kashe kudi, amma sai dai ba a kashe waɗannan kuɗaɗen ba a ma’aikatar harkokin cikin gida da ma’aikatar tsaro ta jihar na shekarar.

 A shekarar 2022, jihar Zamfara ta yi kasafin Naira biliyan 2.3 ga ma’aikatar harkokin cikin gida da kuma na tsaro baki daya, amma sai dai Naira miliyan 994 kawai aka kashe a karshen shekara.

 Daga cikin wannan adadin, gwamnati ta kasafta Naira miliyan 292 domin hidima a shekarar 2022 amma ba ta kashe abinda yakai 0% ba.

 A shekarar 2021 ma’aikatar ta yi kasafin Naira biliyan 2.7 sannan ta kashe Naira biliyan 1.8 a karshen shekara.  A cikin kasafin kudin an ware Naira biliyan 1.2 don kashe kudi, amma babu wani takamaiman aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories