Biliyan 90 Gwamnaton Tarayya Ta Cika A Kuɗin Aikin Hajjin Bana-Shettima

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a yayin ƙaddamar da tashin alhazai na farko da ya gudana a Birnin Kebbi ya bayyana cewa kafin su iya cimma tashin alhazai na bana sai da gwamnatin tarayya ta tayi ciko a aljihun ta.

A cewarsa, “zaku iya tunawa cewa a shekarar da ta gabata, mun fuskanci ƙalubale kafin muka iya samun matsaya akan kuɗin aikin Hajjin shekarar nan.

”Tausayi irin na Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sa ya ɗauki kuɗi Naira Biliyan Chasa’in aka cika don shawo kan matsalar faɗuwar kuɗin mu don tallafawa ‘yan Najeriya baki ɗaya.”

  “Saboda haka, ina kira gare ku kar ku manta yiwa gwamnati addu’ar samun nasara, domin samun zaman lafiya da ci gaban ƙasarmu wanda dukkanmu muke alfahari da ita”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories