Dalilin da yasa bai kamata Musulmi su goyi bayan yajin aikin NLC ba – MURIC

A wani jawabi da MURIC ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta, Farfesa Ishaq Akintola, ta shawarci NLC cewa ta jinkirta yajin aiki har sai bayan Musulmi sun gama bikin sallah.

Wata kungiya mai rajin kare hakkin Musulmai (MURIC) ta sanar da kungiyar kwadago (NLC) cewa yajin aikin da suka shiga zai jefa al’ummar Musulmi cikin mawuyacin hali a yayin da suke shirin tunkarar babbar sallah nan da wasu ‘yan kwanaki.

A wani jawabi da MURIC ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta, Farfesa Ishaq Akintola, ta shawarci NLC cewa ta jinkirta yajin aikin har sai bayan Musulmi sun gama bikin babbar sallah.

“Babu shakka wannan yajin aikin zai jefa rayuwar Musulmi cikin kunci a yayin da babbar sallah ta rage saura kwanaki kadan.

“Kamar yadda al’adar yajin aiki ta ke, dukkan kungiyoyi da ma’aikatu da hukumomi daban-daban sun shiga yajin aiki wanda hakan na nufin rayuwa za ta kara wahala a wurin ‘yan Najeriya a ‘yan kwanakin nan.

DUBA WANNAN: Shettima, Tinubu da matarsa sun kashe N5.2bn a tafiye-tafiye, N12.5bn a kula da jirgi cikin wata uku

“Amma me NLC take tunanin zai faru ga Musulmi a yayin da suke shirin shiga hidimomin babbar sallah? kudin motar da zasu kashe domin yin bulaguro zai tashin gwauron zabi wanda hakan zai shafi zirga-zirga ya kuma ragewa bikin babbar sallah armashi. Wannan shine abinda NLC take so?,” kamar yadda MURIC ta bayyana cikin takardar da ta fitar.

MURIC ta bayyana cewa ba goyon bayan gwamnati take yi ba amma NLC bata shiga yajin aiki a lokacin da ya kamata ba tare da yin kira ga NLC ta sake nazari.

“Muna yin kira ga dukkan shugabannin Musulunci da kungiyoyi Musulmi dake Najeriya akan su yi magana kafin lokaci ya kure. Dole mu yi watsi da wannan yanayi da makiya Musulunci a rigar kungiyanci suka kirkira. Ba zamu yarda da Sallah cikin yajin aiki ba,” a cewar MURIC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories