Cutar Mashako Ta Kashe Mutum 10 A Jigawa, An Samu Kesa-kesai 91

Ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa, ta tabbatar da bullar cutar mashako wato diphtheria a jihar, inda aka samu kesa-kesa a kalla guda 91, yayin da cutar ta kashe mutum 10.

Babban sakataren ma’aikatar, Dakta Salisu Mu’azu shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a garin Dutse ranar Juma’a.

Ya bayyana cewar an tabbatar da kesa-kesai biyu da aka gano a kananan hukumomin Kazaure da Jahun, inda kuma aka tura wasu karin samfuri zuwa Abuja domin gwaje-gwaje.

“Cutar ta fi kamari a wuraren da ba su samu rigafin cutuka a kai a kai,” ya shaida.

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta dauki muhimman matakan da suka dace domin shawo kan lamarin musamman ma bayan samun barkewar cutar a jihohin makwafta kamar Kano da Yobe.

Muazu ya kara da cewa ma’aikatar tana karbar muhimman bayanai daga yankunan da lamarin ya shafa domin daukan matakan gaggawa da sanar da hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa tare da hukumar kula da dakile yaduwar cutuka ta kasa domin neman dauki.

“Gwamnatin jihar a yanzu haka ta maida hankali wajen ganin an samar da rigafi ga jama’a da zarar rigafin ya samu za a dukufa yi wa jama’a,” ya kara shaidawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories