Nesa Ta Fara Zuwa Kusa: Kamfanin BUA Ya Sauke Farashin Siminti Zuwa N3,500

A wani mataki na saukaka wa al’ummar Nijeriya, kamfanin BUA, ya rage farashin Siminti zuwa naira N3,500 a kan kowani buhu, kuma hakan zai fara aiki daga ranar Litinin 2 ga watan Oktoban 2023.

Wannan matakin na zuwa ne a kokarin da kamfanin ke yi na taimaka wa ‘yan Nijeriya musamman kan halin da ake ciki da kuma bunkasa harkokin kayan gini da saukaka farashi.

A kwanakin baya ne dai shugaban rukunin kamfanin Isyaka Rabiu ya ziyarci shugaban kasa Bola Tinubu inda ya sanar da shirinsu na rage karashin simintin. Ya ce, yanzu haka suna kan aikin wasu layuka guda biyu da zai ba su damar suke iya fitar da tan miliyan 17 na siminiti a duk shekara.

A wata sanarwa da kamfanin ta fitar a ranar Lahadi, ta ce, daga yanzu farashin buhun siminti ya koma naira 3,500.

“Dangane da bayanin da muka fitar a baya na niyyar da muke da shi na rage farashin siminti da zarar muka kammala bude sabbin layukanmu a karshen shekara, domin bunkasa kayan gini da sashin gine-gine.

“A cikin yunkurin namu na rage farashin kayayakinmu da sake nazartar ayyukanmu lokaci zuwa lokaci, hukumar gudanarwa na kamfanin BUA tana sanar da abokan cinikayyarmu, da masu ruwa da tsaki hadi da al’umma cewa daga ranar 2 ga watan Oktoban 2023, mun cimma matsayar rage farashin.

“A kan hakan, daga yanzu za a sayar da buhun simintin BUA ne a kan kudi naira 3,500 a buhu guda domin ‘yan Nijeriya su fara cin gajiyar farashin kafin mu kammala tsare-tsarenmu.”

“Idan an kammala aikin sabbin layukan da muke yi, wanda hakan zai kai ga bamu damar zai karin kayan da muke iya fitarwa zuwa tan miliyan 17 a shekara guda, kamfanin siminti na BUA na da niyyar sake dubiya kan farashinmu kamar yadda muka shelanta tun farko zuwa zangon farko na shekarar 2024.”

Kamfanin ya ce, dukkanin simintin da aka yi oda da bai zo ba a halin yanzu, za a sayar da shi ne kan sabon farashin, kuma kamfanin ta gargadi dillali da su tabbatar an bi sabon farashin yayin da suka ce za su bibiyi yadda ake sayarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories